Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Kwayaoyi Dangin su Gyada Bashi da Matsala ga Mata Masu Ciki


Kwayoyin gyada
Kwayoyin gyada

Wani sabon bincike ya karyata maganar da ake yi cewa cin kwayoyi dangin su gyaada yana da lahani ga yaron dake cikin ciki saboda haka masu ciki su gujewa cin su.

Wani sabon bincike ya karyata maganar da ake yi cewa cin kwayoyi dangin su gyaada yana da lahani ga yaron dake cikin ciki saboda haka masu ciki su gujewa cin su.

Wannan sabon bincike ya tabbatar da cewa mata masu cin kwayoyi dangin su gyada ba su sa yaransu cikin wani hatsarin samun damuwa. Binciken ma ya nuna cewa yaran da iyayensu suka ci gyada ba su kan sami matsala wajen cin gyada kamar sauran yara ba.

Dr. Michael Young wani masanin lafiyar yara a makarantar magani ta Harvard da kuma Asibitin Boston, wanda ya jagoranci binciken yace, “Bayanin shine maganar cewa wadanda suka ci wannan kwayar bata narkewa a ciki lokacin da masu ciki suka ci, ba ta da tushe.”

Duk da haka, ya gargadi mata masu ciki da cewar kada su shiga cin yayan kwayoyin yayan itatuwa da kuma su gyada domin kada jikin yayansu ya tashi da kin jinin su

Dr Micheal Young ya fadawa kafar labarai ta Reuter cewa, “Koda yake bincikenmu ya nuna raguwar hatsarin, lallai dole in kara nanatawa cewa daga yadda aka gudanar da binciken, binciken mu ya nuna dangantaka ne kawai.”

Shi da abokan aiki sa sun rubuta a jaridar JAMA cewa tsakanin 1997 da 2010 an sami karuwar matsar sau uku zuwa 1.4 daga cikin dari na yara a Amurka.

Wadanda suka gudanar da wannan binciken sun yi amfani da wani bincike da aka yi akan ma’aikatan jinya mata yan tsakanin shekara 24 zuwa 44. Fara daga shekara ta 1991, matan sukan bada rahoton abin da suke ci.

Daga nan sai masu binciken suka rika kwatanta rahotonnin da suke samu da kuma irin abincin da matan suke ci lokacin da suke da ciki da wani binciken da aka gudanas a kan yayansu.

A shekara ta 2009 matan sun amsa wadansu tambayoyi a rubuce wadanda ke tambayar ko yaransu sun sami wata matsala sakamakon wani abinci da suka ci. Daga cikin yara 8,205, yara 308 ne suka sami wata damuwa bayan sun ci wani abinci, wannan kuma ya hada da yara 104 wadanda suka sami damuwa bayan sun ci kwaya dangin su gyada.

A ciki duka dai, masu binciken sun gane cewa cin kwayoyi dangin su gyada bashi da wata dangantaka da samun damuwa da abinci na yara. A gaskiya ma, yaran matan da suka ci gyada basu cika samun matsala da abinci dangin su gyada ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG