Masanan kimiyya na Amurka sun gano yadda HIV ke kauda shirin kariyar jiki na mutum wanda yake haifas da kanjamau.
Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya tana shirin ayyana kasar Indiya a zaman wadda ta samu nasarar kawar da cutar Polio, ta fita daga jerin Najeriya, Pakistan da Afghanistan.
Wani sabon yaki na neman samar da magunguna masu saukin kudi a kasashe masu tasowa yana nan yana shirin - a wannan lokacin, domin warkar da cutar hepatitis C - fiye da shekaru goma bayan yaki kan kudaden maganin kanjamau a Afirika.
Jihar Kaduna ta doshi kawar da cutar Polio baki daya a bayan da aka shafe shekarar 2013 ba tare da bullar wannan cutar ba
Jami'in na kungiyar Rotary a Jihar Katsina, Muhammad Amin, yace kungiyar ta fii kowane bangare tasiri wajen fadakar da jama'a amfanin yin rigakafin Polio
Zazzabin cizon sauro ya yadu a kasahe fiye da 100 na duniya sai dai kuma za’a iya yi masa kariya ta wajen yin amfani da gidan sauro da kuma fesa maganin sauro domin korar sauron dake dauke da wannan kwayar cutar.
Kokarin da duniya ke yi na kawar da zazzabin cizon sauro, tun daga shekara ta 2000 zuwa yau, ya ceci mutane miliyan 3 da dubu 300.
Mutane kimanin bakwai sun mutu daga cutar kwalara a yankin Badawa - Galedina a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, bisaga bayanin wani shugaban kiwon lafiyar jihar.
Dr. Tijani Husseini, mukadashin direktan kiwon lafiyar jama'a da takaita yaduwar cututuka a ma'aikatar lafiya a jihar, yayi bayani cewa sun fara ganin karuwar masu amai da gudawa makonni hudu da suka wuce. Ya kuma ce, a ka'ida idan aka sami wannan yanayi, duk wanda aka tabatar yana da cutar, sai a bi shi zuwa gida domin tsabtace mahalinshi.
An gudanar da bita ga jami'an kiwon lafiya a jihar Kano a wani kokari na magance aukuwar cutar amai da zawo a jihar. Wasu kungiyoyi masu suna Plenty Health Access Initiative da kuma Community Health and Research Inititiative sune suka hada guiwa domin karawa maikatan lafiya sani a jihar.
Cutar zazzabin cizon sauro na cigaba da addabar al’umma a maradi cikin jamhuriyar Nijar, duk da kokarin da hukumomi ke yi na ganin an shawo kan mastalar.
Malaman lafiya, shugabanin duniya da kuma masu bada taimako daga kewayen duniya sunyi taro domin su tsara taimakon kudi – da kuma su bayyana ci gaban da aka samu a yaki da wadannan cututtukan uku.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.