Dr. Tijani Husseini, mukadashin direktan kiwon lafiyar jama'a da takaita yaduwar cututuka a ma'aikatar lafiya a jihar, yayi bayani cewa sun fara ganin karuwar masu amai da gudawa makonni hudu da suka wuce. Ya kuma ce, a ka'ida idan aka sami wannan yanayi, duk wanda aka tabatar yana da cutar, sai a bi shi zuwa gida domin tsabtace mahalinshi.
An gudanar da bita ga jami'an kiwon lafiya a jihar Kano a wani kokari na magance aukuwar cutar amai da zawo a jihar. Wasu kungiyoyi masu suna Plenty Health Access Initiative da kuma Community Health and Research Inititiative sune suka hada guiwa domin karawa maikatan lafiya sani a jihar.
Cutar zazzabin cizon sauro na cigaba da addabar al’umma a maradi cikin jamhuriyar Nijar, duk da kokarin da hukumomi ke yi na ganin an shawo kan mastalar.
Malaman lafiya, shugabanin duniya da kuma masu bada taimako daga kewayen duniya sunyi taro domin su tsara taimakon kudi – da kuma su bayyana ci gaban da aka samu a yaki da wadannan cututtukan uku.
A yawancin kasashen Afirka baki daya, ana fama da kalubala a fannin wanda yake da hadarin gaske saboda sau da dama ba maida hankali sosai wajen tantance magunguna ko kuma kula da ingancin magungunan wanda ke kawo babban hatsari ga wadanda ke dogara gare su don samun lafiya.
Gwaje-gwajen da aka yiwa mutane domin sanin matsayinsu game da cutar kanjamau ya nuna raguwar yaduwar cutar wanda ya sauko kasa da kashi 1.14 a Abuja, daya daga cikin jihohi sha uku wadanda ada ake lisafta su a matsayin mafyai hatsari, inda kiyascin masu dauke da kwayar cutar ya zarce na kasa baki daya.
Hukumar Kiwon lafiya Tun Daga Tushe ta Najeriya ta ce ganin yadda aka samu nasarar dakile yaduwar kwayar cutar Polio a 2013, ana iya kawar da cutar baki daya nan da 2015
Gwamna Aliyu Mgatakarda Wamakko na Jihar Sokoto yace kudurin gwamnati da na wadanda abin ya shafa ya sa aka cimma wannan tazara
A sabon yunkurin rage cututtukan yara da mutuwar mata a lokacin haihuwa a jihar Benue, fiye da yara miliyan daya da rabi ne wani kamfe da jihar ta shirya ya cimma a zagaye na biyu na makon mata masu juna biyu, jarirai da lafiyar yara da aka kamala kwanannan.
A kammala bayanin hirar da Dr Sambo Sadiku ya yi da wakilin sashen Hausa Abdoulaye Mamman Ahmadu kan raguwar mutuwar kananan yara a jamhuriyar Nijar, Dr Sadiku ya ce ko da yake an sami raguwar mutuwar kananan yara a Nijar amma har yanzu Ana ci gaba da samun mace macen jarirai. Ya ce dalilin da ya sa haka shine rashin nazari akan jarirai.
Yara miliyan 230 ‘yan kasa da shekara biyar a duk fadin duniya ne basu da rijistar haihuwa, wanda ya ke nuna ba lallai su sami ilimi, kiwon lafiya, ko cikakkar kulawa daga gwamnati ba, inji hukumar yara ta majalisar dinkin duniya.
A ci gaba da bayanin Dr Sambo Sadiku kan raguwar mutuwar kananan yara a jamhuriyar Nijar a cikin hirar su da wakilin sashen Hausa Abdoulaye Mamman Ahmadu.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.