Kiyascin mutane biliyan 3.4 zasu cigaba da zama cikin hatsarin kamuwa da cutar yawanci su kuma a kudu maso gabas ta Asia da Africa a inda kashi 80 daga cikin dari na matsalar ke faruwa.
Domin yaki da wannan, kungiyar taimako ta duniya mai yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, kungiyar UNICEF, sashin cigaba na burtaniya da kuma shirin shugaban Amurka sashin zazzabin cizon sauro sun yarda su tanadar da gidan sauro miliyan 200 a watanni 12 zuwa 18 masu zuwa wandanda zasu canji gidajen sauro miliyan 120 su kuma tanada miliyan 80 sababbi.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya tana kuma so ta ci gaba da duba yadda kwayar cutar ke kin jin maganin artemisinin, babban sanadarin dake cikin jansin magungunan da ake kira Artemisin-based combination therapies ko kuma ACT da kuma yadda sauro ke jurewa maganin sauro.
A shekara ta 2013, kasashe hudu a kudu maso gabas ta Asia sun bada rahoton yadda kwayar cutar ta ke kin jin maganin artemisin, kana kuma kasashe 64 sun bada shaidar cewa sauro baya jin magani rahotonnin da ke nuna cewa cin karfin zazzabin cizon sauron da ake tunanin anyi har yanzu bai zauna da gindinsa ba” Inji Dr Robert Newman, Daraktan shirin yaki da zazzabin cizon sauro na WHO a wata hira ta wayar tarho. “Babban kalubalar dake gaban mu bata wani abu bace sai dai ta kudi. Kalubalar ita ce ba mu da isassun kudaden da zau taimaka mana mu ci laggon wannan cutar” inji Newman.