A cikin rahoton ta kan zazzabin cizon sauro na 2013, Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta ce, karuwar kiyayewa da kuma kariya sun taimaka wajen rage mutuwar mutane da kuma zafin ciwon dake da dangantaka da zazzabin cizon sauro. Rahoton y ace, daga cikin milyan 3.3 na rayukan da’aka ceta, yawanci suna cikin kasashe 10 dake da yawan cutar da kuma cikin yara kasa da shekara 5 wadanda sune suka fi kamuwa da wannan cutar.
“Kudaden da aka sa akan kawar da zazzabin cizon sauro, tun daga shekara ta 2007, sun yi aiki sosai” inji Ray Chambers, mai ba sakataren Majalisar Dinkin Duniya shawara akan zazzabin cizon sauro.
Bisa ga rahoton kungiyar kiwon lafiya ta duniya, mutuwar yara ya sauko zuwa kasa da 500,000 a cikin shekara ta 2012.
A gaba daya, cutar zazzabin cizon sauro a shekara ta 2012 wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 627,000, in ji rahoton wanda aka tattaro daga kasashe 102 wadanda ke dauke da zazzabin cizon sauron.
Kiyasin mutane dake dauke da zazzabin cizon sauro bisan kowanne mutum 1,000 dake a hatsarin kamuwa da cutar - wannan kiyashi ya yi la’akari da yawan karuwar jama’a - ya nuna cewa zazzabin cizon sauro ya sauka da kashi 29 cikin dari tsakanin 2000 da 2012 da kuma saukar kashi 31 daga cikin dari a Africa.
A cikin wannan lokacin kuma, mutuwar mutanen dake cikin hatsarin kamuwa da cutar daga cikin mutum 1,000 ya sauka da kasha 45 cikin dari a duniya baki daya da kuma kasha 51 daga cikin dari a cikin yara yan kasa da shekara 5.
Wannan babban cigaban da aka samu bai bude wata kafa ta hutu ba, domin yawan mace macen da ake yi sakamakon zazzabin cizon sauro da kuma yawan kamuwa da cutar basu sauka da sauri kamar yadda ya kamata. Inji Darakta Janar na Ma’aikatar Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Margaret Chan a wani jawabi da ta bayar tare da wannan rahoton.
Chan ta ce, “Hakikanin cewa mutane da yawa suna kamuwa suna kuma mutuwa da zazzabin cizon sauro shine babban abin takaici na karni na 21.”