Nan ba da dadewa ba, gwamna Jonah Jang na jihar Plato zai rattaba hannu akan doka dake kokarin kawar da tsana, kiyayya da kuma bambamcin da ake nunawa mutanen dake dauke da cutar kanjamau.
Ambasadan China a kasar Chadi Hu Zhiqiang ya mika magungunan zazzabin cizon sauro wadanda kudadensu ya kai fiye da kimanin miliyan 680,000 na dalar Amurka ga kamfanin magani na kasar Chadi.
Rahotanni daga Kano sun ce an samu barkewar cutar kwalara har ma an kwantar da mutane fiye da dari a asibiti.
Kwamitin lafiya, sadaswa da wayas da kan jama’a wanda ke karkashin sashen yaki da cutar tarin fuka da kuturta ta jihar Jigawa, ta yi ziyarar wayar da kan jama’a a masarautu biyar a jihar.
Wani dan Majalisar dattawa na Nigeriya, Senato Lee Maeba, ya kalubalanci gwamnatin tarayya domin su maida hankali sosai wajen lura da kokarin kawarda cutar sikari musamman domin gwaji da yin magani.
Yayinda duniya ta kammala ranar ciwon suga ta duniya, an shawarci ‘yan Nigeriya da su dinga yin gwajin cutar kamin ta jawo wata babbar matsala ga jikunansu.
Wani bincike da aka buga a mujalar Lumfashi ta Turai, ta nuna cewa mata masu cutar tarin asma zasu iya samun wahalar daukar ciki wanda zai sa su dauki dogon lokaci kafin su dauki ciki.
Kungiyar lura da ‘yancin ‘yan adam ta gargadi Harare, babban birnin Zimbabwe, kan hadarin sake aukuwar cutar kwalara da ta faru shekaru biyar da suka wuce wadda ta kashe kimanin mutane 4,200.
Masu fama da cutar HIV da ke arewacin Najeriya sun yi amfani da ranar daya ga watan Disamban nan da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da masu cutar wajen bayana halin ko in kular da ake nuna masu a jihar Naija.
Wani sabon bincike ya nuna cewa mutanen da suke yawan cin abincin da ya kunshi kwayoyi masu mai, dangi su gyada da irin su, ba su cika mutuwa daga kansa ko ciwon zuciya ba.
A kowace ranar daya ga watan Disamba a shekara, ana gudanar da bukin ranar yaki da cutar HIV.
Iskar da muke shaka tana hade da abubuwan dake kawo cutar kansa, kuma ya kamata a bayyana su a matsayin masu hadari ga mutane, hukumar lafiya ta duniya ta sashin kansa ce ta bayyana haka.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.