A fadar ma’aikatar bincike da kauda cututtuka (CDC), kimanin mutane 1 cikin 12 a mutanen Amurka suna da asma, wanda ke kiyasce yawan masu cutar a kimanin mutane miliyan 25.
Wani abin da ya sa wannan binciken ya zama da muhimmanci shine mata sun fi saurin kamuwa da tarin asma fiye da maza.
Koda yake an gano dangantakar dake tsakanin rashin haihuwa da tarin asma, wannan sabon binciken ya bada karfi ne wajen dangantakar dake tsakanin tarin asma da kuma jinkirin daukar ciki da ya shafi bincike cikin tagwaye masu yawa.
Masu binciken daga asibitin Jami’ar Bispebjerg ta Denmark, ta dubi sakamakon binciken da aka yi akan tagwaye fiye da 15,000 yan shekaru 12 zuwa 41, wadanda kuma suka amsa jeren tambayoyi game da tarin asma da kuma daukar ciki
Anyi amfani da tagwaye domin binciken don a iya yin kwatanci tsakanin ya da kanwa. Masu binciken sun kuma gane cewa wannan ya ba su damar yin amfani da wani sashin jama’a, daga fannonin rayuwa dabam dabam, ba tare da sai sun gwada irin yanayin su ba ko yanayin irin rayuwarsu.