A madadin karuwar kira domin karin tanada kudin neman maganin cutar kanjamau, an roki gwamnatin tarayya ta juya tanajin kudinta ga sauran cututtuka kamar su kanjamau da ake maida hankali sosai gare shi fiye da cututtuka kamarsu cutar sikari da cututtukan zuciya.
Dan Majalisar Lee Maeba ya bada wannan gargadin a farkon yin bincike na kyauta na cutar sikari wanda wannan kungiyar tayi, Dan Majalisa Lee Maeba da sukayi aikin hadin hannu na wannan kungiyar hadi da ma’aikatar lafiya ta tarayya a Abuja.
Tunda wuri, ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu yace ma’aikatar tana hada hannu da kungiyoyi nagari domin rage wannan cutar ta sikari.
Yayi bayanin cewa fiye da kashi uku na yawan mutuwar wannan cutar sikarin ta faru ne a kasashe masu fama da talauci hadi da Nigeriya.
Dan Majalisa Lee Maeba ya gargadi ‘yan Nigeriya su kauce daga wannan cutar tawurin cin abinci mai nagari, rage shan giya, kauda shan taba, motsa jiki yadda ya kamata da kuma rage shan sikari.