Jihar Naija na da adadin mutane dubu dari uku da hamsin da ke fama da cutar HIV. Wani sugaban kungiyar masu fama da cutar HIV a jihar, Sani Chrisopher Marcus, ya bayana cewa mutane da dama masu fama da cutar HIV suna bukatan kula da kuma taimako mai muhimanci, musamman ta wajen samun abinci da sauran su.
Ita kuma sakatariyar kungiyar mata masu zama da cutar HIV, Angela Layiki, ta fadi cewa ya kamata masu kiwon lafiya da gwamnati gabaki daya su rika sa su a cikin ayukan su na kiyaye wanan cutar.
Uwar gidar gwamnan jihar Naija, Hajiya Jumai Babngida Aliyu, ta baiwa masu cutar gudumuwar kayan abinci kuma ta bayana cewa gwamnati tana abin da ya kamata kuma tana iyaka kokarin ta a wajen kiyaye cutar HIV.