Ghana na cikin kasashe hudu da zasu samu tallafi daga sabon shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, wanda zai lakume karin dala miliyan 10.7 don taimakawa yara masu rauni samun abinci mai gina jiki ta hanyar shirin ciyarwa a makarantu a kasashe kamar Benin, Ghana, Honduras, da Indiya.