Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Da Ke Rikici Da Juna A Kamaru Sun Amince Da Shirin Zaman Lafiya - Canada


Cameroon Crisis
Cameroon Crisis

Ma'aikatar harkokin wajen Canada ta sanar da cewa, gwamnatin kasar Kamaru da wasu kungiyoyin 'yan awaren yankin masu amfani da turancin Ingilishi na kasar, sun amince da fara wani shiri da nufin warware rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 6,000.

Ministan harkokin wajen kasar Melanie Joly, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Juma'a cewa, "Canada na maraba da yarjejeniyar da bangarorin suka cimma na shiga wani tsari na cimma daidaito, cikin lumana da warware rikicin siyasa."

Sanarwar ta ce Canada ta amince da jarjejeniyar da bangarorin suka cimma, tare da kafa kwamitoci don fara aikin gina matakan aminci.

Rikicin makamin da aka fara tun a shekarar 2017, ya samo asali ne daga yadda akasarin masu magana da harshen Faransanci a yankin tsakiyar Afirka, suka mayar da al'ummar Kamaru masu magana da Ingilishi saniyar ware.

Tun daga wannan lokacin ne wasu gungun 'yan awaren ke fafatawa da dakarun gwamnati a yankuna biyu na masu magana da harshen Ingilishi, a kokarinsu na kafa wata kasa ta ballewa mai suna Ambazonia.

Tattaunawar kasa ta 2019 wacce ta ba da matsayi na musamman ga yankuna biyu na Anglophone, ta kasa magance rikicin da ya yi kamari. Kusan mutane 800,000 ne suka rasa matsugunansu, kuma yara 600,000 ba su da cikakkiyar damar samun ilimi, in ji Kanada.

"Wadanda ke cikin wannan yarjejeniya sun hada da Jamhuriyar Kamaru, Majalisar Gudanarwa ta Ambazonia da Rundunar Tsaro ta Ambazonia, Ƙungiyar 'Yancin Afirka da Rundunar Tsaro ta Kudancin Kamaru, da gwamnatin wucin gadi, da kuma tawagar hadin gwiwar Ambazonia. Dukkan bangarorin sun kara bayyana fatan cewa sauran kungiyoyi za su shiga cikin tsarin,” in ji sanarwar.

Mai magana da yawun gwamnati bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba ranar Asabar. An kasa samun masu magana da yawun bangarorin ‘yan awaren domin jin ta bakinsu.

XS
SM
MD
LG