Taron wanda hukumar MDD mai kula da ayyukan jinkai (OCHA) ta shirya shi tare da hadin gwiwar kasashen Norway da Jamus lokaci ne na tattara karin kudaden da za a yi amfani da su domin inganta rayuwar jama’a.
Ganin yadda kura ta lafa sosai a wurare da dama na yankin tafkin Chadi ya sa gwamnatocin kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa da hukumar MDD mai kula da ayyukan jinkai OCHA suka bukaci tallafin masu hannu da shuni domin farfado da harkokin yau da kullum, mafarin bullo da wannan shiri a shekarar 2017 saboda haka taron na Yamai ke farawa da yin waiwaye inji ministan ayyukan jin kan Nijer Alhaji Lawan Magaji.
Jihohin Yobe, Borno da Adamawa ne yankunan da suka dandani kudar matsalolin Boko Haram a Najeriya inda garuruwa da dama suka watse sanadiyar wannan masifa.
Makwafatakar kut da kut da jihohin arewa maso gabascin Najeriya ta yi sanadin yaduwar rikicin Boko Haram zuwa jihar Diffa a nan Nijer inda dubun dubatar mutane suka tsincin kansu cikin yanayin ukuba.
Wakilin sarkin Bosso, Abba Gana Wakil ya zo da shawarwarin da yake fatan ganin taron ya yi la’akari da su in da ya ce ba za a iya mai da jama'a gidanje su, idan har babu abubuwan more rayuwa, kaman su makarantu, asibiti da dai sauransu.
Da yake wani bangare na wannan zama zai maida hankali wajen tattara kudaden dorewar ayyukan da aka sa gaba tuni wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka yi alkaura.
A cewar hukumar raya tafkin Chadi, ‘yan Najeriya sama da miliyan 1 da dubu 900 ne suka arce daga matsugunsu yayin da abin ya shafi wasu mutun dubu 436 a Cameroun sannan a Chadi mutane dubu 312 da ‘yan kai ne suka yi hijira kamar yadda a Nijer abin ya tilastawa mutane dubu 229 da ‘yan kai ficewa daga matsugunansu a wani lokacin da ake fama da matsalolin canjin yanayi.
Saurari rahoton a sauti: