A kokarin kawo karshen aika aikar 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a yankunan kasashen tafkin Tchadi, dakarun kawancen kasashen yankin na can na ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan a baki dayan yankin cikin wani farmaki ba kakkautawa da ma sintiri da ake yi akai akai.
Shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi ya fada a ranar Talata cewa, kungiyar ‘yan tawayen M23 ba ta kammala ficewa gaba daya daga yankunan da ta kwace a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba, yana mai zargin mayakan da yin karya ga yarjejeniyar da aka cimma da su ta janye sojojinta.
Shugaban kasar Nijar ya ba da umarnin daukar duk matakan da suka dace don magance matsalar da ke faruwa a hukumar shige da fice da kuma ma’aikatar haraji ta kasar.
A karkashin jagorancin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, da babban sakataren harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afirka (AfCFTA) Wamkele Mene za a yi taron kan ci gaban Afirka karo na farko a Ghana. Taron da masu ruwa da tsaki suka ce Ghana da Afirka baki daya, za su amfana da shi.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun yanke shawarar rufe wasu kasuwanni a kauyuka da dama na Jihohin Tilabery da Tahoua, da nufin toshe hanyoyin da ‘yan ta’addar arewacin Mali ke amfani da su wajen samun kudaden shiga.
Wata sabuwar dambarwa ta taso a Jamhuriyar Nijar tsakanin ‘yan adawa da masu mulki bayan da shugaban Jam’iyar RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman ya bai wa matarsa mukamin sakatariya a ofishinsa na tsohon shugaban kasa.
Gwamnatin kasar Ghana ta kara wa ma'aikata albashi bayan rashin samun daidaito a yarjejeniyar kara albashi da kashi 60 cikin 100 tsakanin Kungiyar Kwadago da Gwamnatin.
Ma’aikatar cikin gidan Jamhuriyar Nijer ta bayyana shirin fara rajistar kananan makaman da ke hannun farar hula da nufin karfafa matakan zuba ido kan makaman da ke yawo a tsakanin jama’a.
Bayan da Ministan cinikayya da masana'antun kasar Ghana, Alan Kyeremanten ya yi murabus domin cimma burinsa na siyasa, an sake farfado da muhawarar hada shi da mataimakin shugaban kasa Dakta Mahamadu Bawumia a matsayin abokan takara a karkashin jam'iyyar NPP a zaben 2024.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana kasar Uganda a matsayin wacce ta rabu da cutar Ebola, kwanaki 42 tun bayan samun mutum na karshe da ya kamu da cutar.
A ranar Talata ne kasar Zimbabwe ta rattaba hannu kan wata doka da ta haramta zanga-zanga da ma’aikatan kiwon lafiya ke shiryawa, wanda a yanzu za su iya fuskantar tara ko dauri a gidan yari na tsawon watanni shida.
A jamhuriyar Nijer rahoton kungiyar addinin Islama ta kasa wato AIN ya yi nuni da cewa an samu raguwar mutuwar aure a birnin Yamai a shekarar 2022 idan aka kwatanta da adadin aurarakin da suka mutu a shekarar 2021.
Domin Kari