ACCRA, GHANA - Sama da yara ‘yan makaranta miliyan daya ne ake sa ran wannan shirin zai shafa kai tsaye a kasashen Benin, Ghana, da Honduras a wani bangare na kokarin karfafa shirin samarda abinci a makaranta ga miliyoyin yara.
Shirin gidauniyar Rockefeller na shekaru biyu da rabi zai mayar da hankali kan inganta ƙarin abinci mai gina jiki a dukkannin shirye-shiryen yayin da kuma ya jaddada hada samar da isassun abinci cikin makarantu.
Har ila yau, shirin zai tallafa wa ƙananan manoma ta hanyar ƙarfafa gwiwarsu wajen samar da abinci na cikin gida sanna a wayar da kan masu dafa abinci a makarantu game da tasirin abinci mai gina jiki ga yara.
A sanarwar da gidauniyar Rockefeller ta fitar ta bayyana cewa shirye-shiryen ciyar da makarantu za su taimaka wa yara miliyan 388 a duk Duniya. Kuma za su tallafa wa aikin noma na yankuna, kasuwanni, da abinci mafi inganci don samun lafiya, da kuma abinci mai gina jiki, da ilimi a cikin wurare da ake fuskantar talauci.
Manoma a Ghana sun bayyana jindadinsu da ganin cewa shirin zai taimaka wa harkokin nomarsu sosai.
Mallam Jafaru dankwabia mataimakin daraktan binceken yanayi da kare martabar abinci ya ce, idan aka bi dukkan sako da manoma suke sai aka hadasu da masu harkar shirin bayar da abinci a makarantu ko masu dafa abinci zai rage wahalar da manoma ke sha don ganin sun kai kayan gonansu cikin gari.
A Shirin Na Samar Da Abinci a Makarantun, ƙungiyar ƙasashe 73 ta himmatu wajen tabbatar da cewa nan da shekara ta 2030 kowane yaro a duniya ya samun abinci mai gina jiki na yau da kullun a makaranta,da zai ci gajiyar wannan sabon shirin na karin dala $10.7.
Saurari ciakken rahoto daga Hawa AbdulKarim: