Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TOGO: An Kammala Taron Kasa Da Kasa Da Nufin Kawar Da Ta'addanci A Nahiyar Afrika


TARON DAKILE TA'ADDANCI A NAHIYAR AFRIKA
TARON DAKILE TA'ADDANCI A NAHIYAR AFRIKA

An gudanar a taron neman hanyar yaki da ta'addanci a kasashen nahiyar Afrika da ya samu halartan kungiyoyin matasa da wakilan majalisu da shugabanninsu tare da wasu jami'ai na Majalisar Dinkin Duniya.

Yayin taron, an kafa kungiyar hadin kan wakilai a Majalisun Nahiyar Afrika da zata rinka tinkarar matsalar tsaro musamman na ta'addanci

Yayin jawabinta , shugabar Majalisan Dattawan kasar Togo, Yawa Djigbodi Segan, tace hare -haren ta'addanci na barazana sosai ga cigaban nahiyar Afrika kuma matakin soji kadai ba zai iya shawo kan matsalar ta'addanci a Nahiyar Afrika ba sai an hada kai tare da tinkarar matsalolin da matasa ke fuskanta.

TARON DAKILE TA'ADDANCI A NAHIYAR AFRIKA
TARON DAKILE TA'ADDANCI A NAHIYAR AFRIKA

A hirar shi da Muryar Amurka, jigo a majalisan dattawa ta kasar, Ghana James Agalga da ya wakilci Ghana a taron yace:

"mun tattauna akan gudunmuwar da wakilai a Majalisun sassan nahiyar Afrika zasu bayar wajen kawar da ta'addanci a nahiyar. Mun kuma tattauna kan matsalar rashin sana'a a nahiyar tare da gudunmuwar da matasa za su bayar wajen shawo kan wannan matsala sabida akasarin al'umman nahiyar Afrika matasa ne kuma matsala babba da ke addaban su shine rashin sana'ar yi".

TARON DAKILE TA'ADDANCI A NAHIYAR AFRIKA
TARON DAKILE TA'ADDANCI A NAHIYAR AFRIKA

Mai sharhi bisa harkan tsaron ciki da wajen Ghana Irbad Ibrahim ya bayyana cewa ko shakka babu wannan matakin tinkarar matsalolin da matasa ke fama dashi yayi tasiri sosai a kokarin da a ke yi wajen shawo kan wannan matsala. Irbad Ibrahim ya kuma bukaci a kara shugabannin addinai a ciki tare da samar musu da tallafi sabida suna da murya sosai.

Majalisar Dinkin Duniya da Majalisar Shurad ta kasar Qatar tare da gwamnatin Togo suka shirya wannan taro na wuni biyu a kasar Togo.

XS
SM
MD
LG