Hambararren shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, wanda ake tsare da shi a gidansa tun bayan hambarar da shi a makon da ya gabata, ya samu 'yancin zai kuma iya tafiya kasar waje don neman duba lafiyarsa, a cewar gwamnatin mulkin sojan kasar yayin da take nada sabon firaminista.