NIAMEY, NIGER - Bayanan da hukumar ‘yan sanda ta ce ta samu daga wurin da ake zaman dirshan din da wasu kungiyoyin fararen hula suka shirya don tilasta wa sojojin Faransa ficewa daga Nijar sun bayyana cewa wasu mutane na amfani da wannan dama domin cin zarafin jama’a.
Dalili kenan da ya sa shugaban hukumar ‘yan sandan birnin Yamai Janar Abdoulsalam Adam Mahaman ya ziyarci inda ake wannan taro don jan hankali akan maganar bin doka da oda.
Ya ce akwai bukatar a janye daga hanya domin akwai wadatacen filin da zai iya daukar masu zanga-zangar. Ya ce sun samu rahoton cin zarafi har ma da aikata fyade, koda yake babu dadin fada.
Kuma tuni a cewarsa, sun kama wasu mutane akan wannan laifi, ya ce za su ci gaba da aiki saboda haka ya zama wajibi mutane su taimaka musu.
Hukumar ‘yan sandan ta ce ta lura da yadda wasu ke uzurawa masu ababen hawa.
Ya ce "mutum na isa da motarsa za ka ga sun umurce shi ya sauke gilashi, ana ta bubbuga mota sannan a umurce ka fidda belt idan kuma babur gareka a ce ka fidda hular kwano. Ai canjin mulki ba ya nufin kowa ya yi abin da ya ga dama ba. Saka belt da dora hular kwano abu ne na bin doka saboda haka ya zama wajibi mutane su kiyaye doka."
Da yake maida martani kan abubuwan assha da hukumar ‘yan sanda ta ce suna wakana a wurin da ake zanga-zangar nuna adawa da zaman sojan Faransa, wani kusa a gamayyar kungiyoyin da ke jagorancin wannan fafutika Bana Ibrahim ya ce za su karfafa matakai.
Tun a ranar farkon kaddamar da zaman farko ne ‘yan kasa suka yi ta gargadi dangane da munanan abubuwan da ka iya biyo baya. Jan hankulan da hukumar ‘yan sanda ta yi abu ne da ya farfado da mahawwara akan halacci da ma salon gudanar da wannan taro.
A ranar Juma’a 1 ga watan Satumba ne mazaunan birnin Yamai suka fara tarewa a harabar sansanin sojan Faransa don yin zaman dirshan na sai yadda hali ya yi, da nufin amsa kiran kungiyoyin fararen hular da ke gwagwarmayar ganin Faransa ta kwashe dakarunta daga Nijar bayan shudewar wa’adin 2 ga watan Satumba da Majalisar sojojin da suka yi juyin mulki ta diba wa sojan na Faransa don su fice.
Saurari ciakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna