Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar CODDAE Ta Kudiri Aniyar Maka Najeriya A Kotu


Taron Gamayyar CODDAE
Taron Gamayyar CODDAE

Kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi mambobin gamayyar CODDAE A Jmhuriyar Nijer sun kudiri aniyar shigar da kara a gaban kotu saboda zargin Najeriya da yin fatali da yarjejeniyar kasuwancin da ke tsakaninta da Nijer a fannin makamashi.

Najeriya ce ke bai wa Nijer Kashi 70 daga cikin 100 na wutar lantarkin da jama’ar kasar ke bukata sai dai gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta katse wutar a wani bangare na takunkumin kungiyar CEDEAO biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, matakin da ‘yan fafutika suka ce ya saba wa doka dalili kenan suka kudiri aniyar garzayawa kotu kamar yadda jagoransu Alhaji Moustapha Kadi ya bayyana a taron manema labaran da suka kira.

Alhaji Moustapha yace ya zama wajibi jama’ar kasa da na duniya baki daya su sani duk da yake shugaba Bola Ahmed Tinubu na da ‘yancin katse wutar da kasarsa ke ba Nijer to amma matakin ya saba wa yarjejeniyar da ta shimfida wannan haraka sabili kenan gamayyar CODDAE ta lashi takobin kai koke a gaban kotu domin ta kwato wa ‘yan Nijer hakkinsu sai dai kawo yanzu ba su saka ranar shigar da karar ba.

Matakin na Tarayyar Najeriya ya haddasa tsayawar al’amura a fannoni da dama inda ‘yan Nijer ke tafka asarar dimbin kudade a kowace rana alhali tun kafin a girka ECOWAS kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar kasuwancin wutar lantarki.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG