An nada masanin tattalin arziki, Raymond Ndong Sima, a matsayin "firaministan rikon kwarya," a cewar wata sanarwa da kakakin kwamitin mika mulki, Col. Ulrich Manfoumbi ya karanta a gidan talabijin na kasar.
Sima, mai shekaru 68, ya taba zama firaminista a karkashin hambararren shugaban kasar daga shekarar 2012 zuwa 2014, kuma ana kyautata zaton zai yi burin shiga zaben. Sai dai bai zama dan takarar jam'iyyar adawa ba a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Afirka ta Tsakiya.
Kanar Manfoumbi ya kuma fada a ranar Laraba cewa, hambararren shugaban "ya samu 'yancin sa la'akari da yanayin lafiyarsa." "Yana iya, idan ya ga dama, ya fita kasar waje don duba lafiyarsa," in ji shi.
Har yanzu dai ba a bayyana lafiyar jiki Ondimba ba. Ya yi fama da bugun jini a karshen shekarar 2018 wanda ya hana shi yin aiki na tsawon watanni. Gidan talabijin na cikin gida Gabon24 ya watsa wata ganawa da yammacin Laraba tsakanin Ondimba da Abdou Barry, shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya na Afirka ta Tsakiya.
"Na same shi cikin koshin lafiya," in ji Barry game da ganawarsa da hambararren shugaban.
An dai hambarar da Ondimba mai shekaru 64 a duniya a ranar 30 ga watan Agusta ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun juyin mulki a wasu sassan Afirka. Jim kadan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ta cece-kuce da zai tsawaita wa'adin mulkin danginsa na shekaru 55. Ya gaji mahaifinsa Omar Bongo a shekara ta 2009.
A halin da ake ciki kuma, sabon shugaban mulkin sojan da aka rantsar a Gabon, Janar Brice Clotaire Oligui Nguema, ya gana da hukumomin yanki da na kananan hukumomi a cikin wannan mako, inda ya yi alkawarin samar da ingantattun ababen more rayuwa da mika mulki cikin lumana ga 'yan kasar a kasa mai arzikin man fetur ta Afirka ta Tsakiya.
Ana ci gaba da nuna damuwa game da yadda sojoji suka karbe mulki da kuma jinkirin dawowar mulkin dimokradiyya a sassan Afirka inda sojoji suka yi alkawarin mika mulki na tsawon lokaci. Sabon shugaban mulkin soja a Gabon ya kuma yi alkawarin mayar da mulki ga al'ummar kasar ta hanyar shirya zabe cikin gaskiya da adalci amma bai bada wa'adin kada kuri'a ba.
Dandalin Mu Tattauna