‘Yan siyasa da jami’an fafutuka a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da Firai Ministan Gwamnatin rikon kwaryar kasar ya sanar cewa Gwamnatin da soja suka hambarar a watan Yulin da ya gabata ta ci dimbin bashi daga ciki da wajen kasar.
Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijer ta bayyana cewa ta tarar da tarin bashin dubban billion cfa da hambararriyar gwamnatin kasar ta ci galibi daga kasashen waje.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin ta bukaci dala biliyan 1 don taimaka wa wadanda ke gudun hijira a Sudan, inda ta ce tana sa ran sama da miliyan 1.8 za su tsere zuwa kasashe makwabta biyar a karshen shekara.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar sake bude sararin samaniyar kasar ga wani rukunin jiragen sama da nufin bai wa matafiya damar zirga-zirga tsakanin kasar da sauran kasashen duniya.
A ranar 30 ga watan Agusta, mintuna kadan bayan sanarwar Bongo ya lashe zabe, sojoji karkashin jagorancin Janar Oligui Nguema ya karbe mulki.
Dubban mazauna birnin Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan Faransa da zummar tilasta wa gwamnatin shugaba Macron kwashe wadannan sojoji daga kasar ta Nijer.
Mataimakiyan sakatarin harkokin wajen Amurka mai kula da sha'anin Afrika Molly Phee ta bayyana cewa Ghana da Amurka za su ci gaba da hada hannu wajen tabbatar da mayar da dimokradiyya a Nijar.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da jandarmomi sun dukufa da binciken motocin da ke fitowa daga ofishin jakadancin na Faransa da wadanda ke fitowa daga gidansa a Yamai.
Babbar kungiyar ‘yan adawar kasar Gabon, Alternance 2023, ta yi kira ga kasashen duniya a yau Juma'a da su karfafa wa gwamnatin mulkin da ta hambarar da shugaba Ali Bongo kwarin gwiwar ta mika mulki ga farar hula.
A cewar mai sharhi kan al’amuran siyasa, Rotimi Olawale, juyin mulki na bazuwa a nahiyar Afirka ne saboda masu rike da madafun iko sun gaza wajen tabbatar da wanzuwar tsarin dimokardiyya mai inganci.
A ranar Alhamis kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Gabon daga zama mambar kungiyar, kwana guda bayan hambarar da shugaban kasar Ali Bongo.
Gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar soke dukkan wasu abubuwan alfarma ga koreren jakadan Faransa Sylvain Itte da iyalinsa sakamakon shudewar wa’adin da aka ba shi domin ya fice daga kasar.
Domin Kari