NIAMEY, NIGER - Wannan al’amari na faruwa ne a wani lokacin da gwamnatin Emmanuel Macron ta yi watsi da bukatar ficewar jakadanta daga Nijar a yayin da zanga-zangar adawa da zaman sojojin Faransa a kasar ke gudana a wuni na shida a harabar sansaninsu da ke birnin Yamai.
A sanarwar da suka bayar ta kafar talbijin ta RTN mallakar Gwamnati ne hukumomin kasar suka ce a binciken da jami’an tsaro suka yi a wata mota dab da shigarta ofishin jakadancin Faransa da misalin karfe 7:30 na yammacin jiya Talata, an gano wasu kakin soja kimanin 16 masu tambarin rundunar sojojin Burkina Faso hade da takalman soja guda biyu.
Motar da aka gano wadanan kayayyaki na dauke ne da kayan daki dangin gadaje da kwabobi mallakar wani sojan Faransa da ya tashi daga gidan da yake haya da nufin tarewa a ofishin jakadancin na Faransar a cewar wannan sanarwa.
A ra’ayin Shugaban kungiyar Voix des Sans Voix, Nassirou Saidou faruwar wannan al’amari a dai-dai lokacin da dangantaka ke kara tsami a tsakanin Nijar da Faransa manuniya ce da ke fayyace girman bukatar tsauraran bincike.
Sai dai Shugabar kungiyar ABC ta masu fafutika ta yanar gizo wato Blogeur Madame Samira Sabou ta ce binciken da ta gudanar akan wannan batu na nunin sojan da ake magana akansa ya yi aiki a ofishin jakadancin Faransa a Burkina Faso a baya.
Haka kuma akwai tarin ayoyin tambayar da ya zuwa yanzu ba za a iya bada amsa akansu ba inji Samira.
A ranar 25 ga watan Agustan da ta gabata ne Gwamnatin rikon kwaryar Nijar ta bai wa jakadan Faransa Sylvain Itte wa’adin awoyi 48 ya fice daga kasar, umurnin da Gwamnatin Macron ta yi watsi da shi mafari kenan jami’an tsaron Nijar suka kaddamar da binciken motocin da ke shiga da fita a ofishin jakadancin Faransa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna