Aljeriya ta fitar da Nijar da takwarorinta na kasashen Mali da Burkina Faso daga jerin kasashen da ke cin gajiyar shirinta na raya kasashensu bisa zargin su da neman kusanci da Maroko da basa jituwa da juna.
Jagoran sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi wa wasu firsinoni afuwa bisa la’akari da sharudan da dokokin shari’ar kasar su ka tanada, matakin da jami’an kare hakkin dan adam suka yi na’am da shi ganin yadda abin zai taimaka a rage cunkoso a gidajen yari.
Duk tawagar da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 za ta samu kyautar dala miliyan bakwai ($7M), kwatankwacin (Yuro Miliyan 6.4), kamar yadda Hukumar Kwallon Kafar Afirka ta CAF ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Nijar ta bayyana aniyarta na karfafa cinikayya da kasashe makwabtanta irin su Aljeriya da Libiya, ta yadda za ta yi amfani da tashoshin jiragen ruwan kasashen domin shigo da kayayyaki daga ketare ko kuma fitar da kayan kasar.
Karawar karshe ta gasar ta bana an yi ta ne tsakanin Kadiri Abdou wanda aka fi sani da Issaka Issaka, dan kokawar jihar Dosso da kuma Mati Souley na jihar Maradi, inda Kadiri Abdou ya sami nasara, ya kuma sake daukar takobi.
A yayin da ake ban kwana da shekarar 2023 kuma ake marhaba da sabuwar shekara 2024, akwai wasu muhimman abubuwa da suka faru a bangarori daban-daban a kasar Ghana, wadanda suka hada da siyasa da tattalin arziki da ilimi da sauransu. Haka kuma kasar ta yi alhinin mutuwar wasu fitattun mutane.
A cikin watannin 12 da suka gabata, shugabannin Afirka sun ziyarci hedkwatar Tarayyar Turai a Brussels da Indiya da Rasha da Amurka da Saudiyya da Afirka ta Kudu da kuma Turkiyya.
‘Yan sanda sun yi dafifi a babban birnin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo a yau Laraba da shirin dakile duk wani tashin hankali da jam’iyyar adawa zata tayar a game da babban zaben kasar da aka gudanar a makon da ya gabata.
Rahoton hukumar CONOREC ya bayyana cewar fiye da kaso 63 cikin 100 na sama da masu kada kuri’a milyan 8.3 a kuri’ar raba gardamar data gudana a ranar 17 ga watan Disamba.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a tsakiyar Congo da ta yi sanadin mutuwar mutane 22, cikin har wasu iyalan gida daya su 10, kamar yadda wani jami’in yankin ya bayyana a ranar Talata.
Domin Kari