Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Tsohon Dan Adawar Chadi Succes Masra Fira Minista


Shugaban Transformers Party kuma sabon Fira Ministan Kasar Chadi, Dr Succès Masra. (VOA/André Kodmadjingar)
Shugaban Transformers Party kuma sabon Fira Ministan Kasar Chadi, Dr Succès Masra. (VOA/André Kodmadjingar)

A wani labari da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito a yau Litinin, Shugaban wucin gadi a Chadi, Mahamat Isriss Deby Itno, ya nada tsohon shugaban jam’iyyar adawar kasar wanda bai jima da komawa kasar ba a matsayin Fira Minista

Shugaban Transformers Party, Success Masra, wanda ya dade yana adawa da mulkin Shugaba Deby wanda ba da jimawa ba ya koma Chadi daga inda yake buya a watan Nuwamba bayan cimma yarjejeniya da shugabannin mulkin sojin kasar.

Kwanaki kafin kuri’ar neman jin ra’ayin jamma’a da akayi a kasar a watan da ya gabata, wanda sakamakonsa ya nuna kaso 86% na ’yan kasar da suka kada kuri’a sun amince da yiwa kundin tsarin dokokin kasar kwaskwarima, Masra ya bukaci magoya bayan shi su amince da bukatar inda ake sa ran cewa sakamakon zaben zai bada dama a gudanar da zabe a kasar.

An nada “Dakta Succes Masra” a matsayin Fira Minista, wanda zai jagoranci al’amuran mika mulki ga sabon gwamnati, babban sakataren gwamnatin Shugaba Idriss Deby ya sheda ta kafar talabijin na kasar.

Masra ya ketara kasar waje inda ya shiga buya jim kadan bayan boren da aka yiwa gwamnatin sojin kasar wanda ta zarce wa’adin wattani 18 din da ta dibawa kanta don gudanar da zabe da kuma mika mulkin ga zababen farar hula na ranar 20 ga watan Oktoban 2022.

A ranar 3 ga watan Nuwamban bara ne Masra ya koma gida biyo bayan sanya hannu akan wata yarjejeniyar daidaita tsakani a birnin Kinsasha a ranar 31 ga watan Oktoba wanda zata bashi damar gudanar da ayyukansa.

Ya fada wa gwamnatin cewa yana fatar a ci gaba da samun tattaunawa tsakani da zummar warware matsalar cikin lumana .

Jam’iyyun adawa da dama sun nesanta kan su da Masra yayin da a bangare guda suka ci gaba da sukar yafiyar da gwamnatin ta yiwa duk ‘yan Chadi fararen hula da sojoji da ke da hannu a boren na watan Oktoban 2022 wanda aka lakabawa Bakar Laraba ko kuma ''Black Thursday'' a turance.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG