'Yan Sandan sun hallara a Kinsasha ne don tarwatsa duk wani bore da aka shirya yi bayan da Jam’iyyun adawa suka ki amincewa da zaben da suke ganin anyi aringizo
Gwamnatin kasar ta haramta zanga-zangar da ake shirin yi a Kinsasha tana mai cewa an kitsa yin boren ne don bata tsarin zabe.
Masu kada kuri’a sun fuskanci jinkiri sannan a wasu wurare sun kasa kada kuri’un su sakamakon cewa turawan zabe sun gaza kai kayayakin zabe wuraren zabe.
An kara wa’adin kada kuri’a da zummar shawo kan matsalolin, sannan a wani bangare kuma don sukar jam’iyyar adawa da rashin tsarin da dokokin kasa ya shimfida.
Sakamakon wasu kuri’un da aka bayyana ya zuwa yanzu na nuni da cewa, shugaba Felix Tshisekedi ne ke kan gaba da akalla kuri’u kaso 79% daga kuri’u miliyan 6.1n da aka kirga.
Mutane miliyan 44 ne suka yi rajista.
Dandalin Mu Tattauna