Da yake jawabi lokacinda ya karbi bakuncin ‘yan jarida da wadansu shugabannin addinin kirista a lokacin bude bakin watan Ramadan, Mai alfarma Sarkin Musulmin yace yanayin da Najeriya ke ciki a halin yanzu, babbar kalubala ce dake bukatar hada hannu. Musamman domin samarda sauyi mai ma’ana ,tare da shawo kan kashe kashen rayuka dake addabar kasar.
Yace a can baya, mun yi ta da’awar canji, yanzu canjin ya tabbata, sai dai canjin bai tsaya a zabe kadai ba.wajibi ne mu kara harama wajen tabbatar da canjin da muke bukata. Sarkin Musulmin yace aiki yana gaba tukuru inda ake bukatar hada karfi domin ciyar da kasar gaba.
Mai martaba sarkin Musulmin ya kuma yi kashedi a kan hadarin dake tattare da kalaman wadansu shugabanni musamman na addini da suka shafi zargin juna da kuma yin suka da aiki tare da ake yi tsakanin mabiya addinin Kirista da Musulmi domin samun fahintar juna.
Yace lamrin yafi Kamari a Arewa, kuma wadannan kamalan na shugabannin yankin ba alheri bane. Ina gani lokaci ya yi da zamu zauna mu kawo karshen wannan matsalar, domin kuwa a wajen tarukanmu mukan yi kalamai kyawawa, to amma sai kaji wadansu a kafafen watsa labarai suna wadansu kalamai na dabam.
Shima a nashi bayanin. Pastor Yohanna D. Buru, yace gudanar da zabe lami lafiya alamace cewa talakawa sun ji kiran da shugabannin addini suka yi masu. Yace ba a rabuwa da bara gurbi tsakanin mabiya addinai ko kabila ko kuma al’umma, sai dai yace abinda yafi muhimmanci shine, dukan mabiya addinai sun bincika ko abinda suke yi yayi daidai da koyarwar addininsu ko babu.
Pastor Buru yace, abinda kawai suke gudu shine, kada abinda suke yi ya sabawa addini, amma muddar bai sabawa addini ba, to zasu ci gaba da aiki sai inda karfinsu ya kare.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya hada mana.