Tsohon gwamnan farin kaya na farko a jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha ya rasu jiya a asibitin koyarwa na jami’ar Patakwal sakamakon bugun zuciya.
Masu kada kuri’a sun yi layi a kasar Guinea yau lahadi da safe domin zaben shugaban kasa, inda shugaban kasar Alpha Conde ya sake tsayawa takara domin neman wa’adin mulki na biyu, tare da ‘yan takarar jam’iyun hamayya bakwai.
Hukumomi a kasar Chadi sun ce a kalla wadansu mata ‘yan kunar bakin wake biyar suka kai hare hare a wadansu wurare biyu kusa da kan iyakar Najeriya suka kashe a kalla mutane 33 da suka hada da ‘yan asalin kasar Chadi da kuma ‘yan Najeriya dake gudun hijira a kasar.
Hukumar lafiya ta duniya tayi kira ga gwamnatoci su kare ‘yancin al’ummarsu dake da tabuwar hankali wadanda ake fuskantar wariya da kuma kuntatawa.
A kalla mutane tamanin da shida suka rasu yayinda maitan kuma suka jikkata a tagwayen fashe fashen da suka auku a babbar tashar jirgin kasar Turkiya
Masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya a Najeriya sun kudiri aniyyar daukar matakan hana sake bulluwar cutar Shan Inna da ake kira Polio a turance, bayan da hukumar lafiya ta aiyyana Najeriya a matsayin kasar da ta rabu da cutar Polio.
Yayinda Mataimakin shugaban kasa Farfes Yemi Osinbajo ke cewa gwamnati na sane da yadda kamfanonin wutar lantarki ke tatsar masu amfani da wutar, Talakawa a kasar na cigaba da kokawa,
A cikin watan da ya gabata ne dai Boehner ya bayyana cewa zaiyi murabus daga shugabancin majilisar
NATO zata yi taron ministocin tsaro a Brussel ana sa ran batun rawar da Rasha ke takawa akan yakin da akeyi a kasar Syria ya mamaye batun da za'a tattauna
Babban kotun kasar Rwanda ta baiwa shugaba Paul Kagame damar sake tsayawa takaran shugabancin kasar
Yanzu haka dai ana kan gumurzu a cikin birnin Kunduz
Domin Kari