Shugaban NATO ya caccaki kasar Rasha game da batun ayyukan kasar ta Syria, wannan ko na faruwa ne kwana daya bayan Moscow ta kaddamar da hari a matsayin wani bangare na karfafa yaki da take yi ta sama akan yan tawayen Syria.
Jens Stoltenberg yayi wadannan kalamun ne dai yau din nan sailin da ya isa wajen taron da NATO zata yi taron ministocin tsaro a Brussel, inda a wajen wannan taron ne ake sa ran batun rawar da Rasha ke takawa akan yakin da akeyi a kasar ta Syria ya mamaye batun da za a tattauna a wannan taron.
Wannan batu yana da dinbin tasiri musammam ma bayan da rahotanni a cikin wannan sati suka bayyana cewa jirgin yakin Rasha da yakai hari a Syria yaketa sharuddan anfani da sararrin samaniyar kasar Turkiyya.
Stoltenberg yace NATO tana da karfi da kuma shirin da zata iya kare duk wanda ya dace ta kare ciki ko har da Turkiyya.
NATO Tace tuni ta mayar da martini musammam ma wajen kara karfi, da kayayyakin da suka dace ciki ko harda sojojin da suka kai kudancin kasar da kuma turkiyya.