Ko da yake an sami fito na fito tsakanin magoya bayan jam’iyun dake hamayya da juna a farkon makon nan, a kasar Guinea, babu alamar rikici a Conakry lokacin da aka bude runfunan zabe.
Sai dai jam’iyun hamayya sun fara korafi kan zaben. A wata hira da babban shugaban jam’iyar hamayya Cellou Dalein Diallo ya shaidawa muryar Amurka cewa, bai amince da hukumar zaben ba. Yace shi da sauran ‘yan takarar shida zasu ki amincewa da sakamakon zaben idan har suka hakikanta cewa, an tafka magudi.
Dialo yace idan sakamakon zaben da hukumar zabe ko kuma kotun koli suka sanar, suka sabawa abinda jama’a suka zaba, ba zai amince da shi ba.
Jama’a sun shiga layi cikin tsanaki a mazabar unguwar Minierre dake birnin Conakry, inda wata jami’ar zabe tace zaben yana tafiya yadda ya kamata