A watan jiya ne hukumar ta kiwon lafiya ta duniya ta fitar da Najeriya a jerin kasashen da ke fama da Shan Inna. kafin wannan furucin Najeriya ce kasa daya tilo dake fama da kwayar cutar Polio a nahiyar Afrika, lamarin da ya janyo wa kasar koma bayan tattalin arziki saboda yawaitar nakasassu a kasa.
A cewar Jami'i mai kula da allurar rigakafi a jihar Plato, Malam Sani, kokarin da hukumomi su ka yi wajen wayar da kan al'umma akan cutar Polio ya taimaka wajen kawas da cutar. ya kuma ce har yanzu kofofin bada rigakafin cutar Polio da gwajin cutar na nan a bude.
Kwadinetan cibiyar samar da kekuna ga guragu da ake kira Beautiful Gates Handicaped Center a turance, Mr. Ayuba Gofan wanda shi ma ke da nakasa sanadiyyar cutar ta Polio. Ya ce wannan cibiyar an kafa ta ne don taimakawa nakasassu da suka rasa kafafunsu sanadiyar cutar Polio, ya kara da yin kira ga gwamanti da ta sa hannu a al'amuran nakasassu (musamman sanadiyar cutar Pollio), ta fannin ilimi, koyon sana'a da kuma duk wani tallafi da gwamnati zata iya badawa don su zama masu dogaro da kansu.
Shi ma wani nakasasshe sanadiyar cutar Polio da aka sakaya sunansa, yace bai taba bara ba a rayuwarsa don bara ba abin yi ba ce, akwai sana'o'i da yawa da nakasassu za su iya yi. A nasa ra'ayin mutuwar zuci ke sa bara. kuma yayi kira da nakasassu da su tashi su nemi na kansu.
A cewar mataimakin limamin baban masallacin Jos, Mohammed Gazali Isma'il Adam, Jama'a su cigaba da bada goyon baya ga gwamnati wajen kai 'yayansu rigakafin cutar Polio.
Ga karin bayani daga Zainab Babaji.