Gwamnatin jihar Filato ta ce ta bullo da wani sabon tsari na fadakar da al’umma kan su sanya ido kan makwabtansu, don gano wadanda ke fakewa suna kashe mutane da yin garkuwa da su.
Wasu hare-hare a kauyen Dong dake kan iyakar kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa, sun yi sanadin rasa rayukan mutum biyar a yammacin ranar Asabar.
Dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a jahar Filato sunyi nasarar hallaka wasu masu garkuwa da mutane su uku, suka kuma kwace makamai.
Hukumar ta NCDC ta ce mutum dari da biyu ne suka mutu da cutar ta Lassa a Najeriya a bara.
Jihar Filato ta sha fama da matsalolin hare-haren da kan kai ga asarara rayuka da dumbin dukiyoyi.
Wani sabon rikici tsakanin al’ummomin Tibi da Fulani a kananan hukumomin Lafiya da Obi a jihar Nasarawa, ya yi sanadin rasa rayuka da dama.
Majinyata a asibitin kwararru a jahar Filato sun shiga hali mara dadi, bayan daukacin ma’aikatan dake asibitin, in banda likitoci, suka shiga yajin aiki na sai yadda hali yayi.
Hukumar gidan gyara hali dake jahar Filato ta tabbatar da hari da ‘yan bindiga suka kai wa gidan yari.
Kungiyoyin kwadago na cibiyoyin bincike a Najeriya sun bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ceto cibiyoyin daga durkushewa, saboda halin tagayyara da cibiyoyin ke ciki.
Rahotanni sun ce tun da safiyar ranar Alhamis aka tsaurara matakan tsaro a kewayen majalisar, wani abu da ya yi nuni da cewa akwai abin da ke faruwa.
Kungiyar Fuiani makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders, shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya ta gudanar da gagarumin taro a garin Lafiya, jihar Nasarawa don jan hankalin Fulani su yaki jahilci ta hanyar sanya ‘ya’yansu a makarantun addini da na zamani.
Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce sojin Najeriyar za su ci gaba da aiki tare da gwamnatin Jihar Filato don maido da zaman lafiya da tsaro a cikin jihar.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da mutum goma a gaban babban kotun jihar Filato wadanda take zargi da hannu a kisan wasu matafiya a Rukuba Road kan hanyarsu zuwa jihar Ondo.
Kungiyar al’ummomin dake jihohin tsakiyar Najeriya wato Middle Belt Forum ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayan wadanda ke tallafawa kungiyar Boko Haram.
Mai martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya jaddada cewa duk wadanda ke daukan makami suna kisan jama’a da sunan addini, zasu fuskanci mummunan hukunci daga Allah.
“Akwai bukatar a kara mayar da hankali wajen tabbatar da doka da oda da kuma sake gina tubalan zaman lafiya,” a tsakanin al’uma.
Al’ummar kauyen Yalwan Zangam a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato na zaman fargaba da tashin hankali bayan da ‘yan bindiga suka shiga kauyen a daren ranar Talata suka hallaka maza da mata da yara kanana.
Dakarun Najeriyar sun kashe 'yan bindigar ne bayan da suka halaka wasu 'yan sanda uku masu farin kaya, wadand suka je bincike a yankin karamar hukumar Mangu.
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam a Jihar Filato ta ce ba ta ba kowa ko wata kungiya damar gudanar da wani tattaki ko zanga-zanga a harbar babban masallacin da ke birnin Jos ba.
Domin Kari