Shugaban kungiyar, reshen jahar Nasarawa, Alhaji Bala Mohammad Dabo ya ce sun tattauna ne kan hanyoyin magance matsalolin rashin zaman lafiya tsakaninsu da manoma.
Ya kara da cewa sun ja hankalin al’ummar Fulani da su sanya ‘ya’yansu a makarantu don yakar jahilci dake sanya su shiga wadansu halaye da ba su dace ba.
Yahaya Musa Jibrin dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Gindin Akwati dake karamar hukumar Barkin Ladi a jahar Filato, ya ce kungiyarsu tare da hadin gwiwan jami’an tsaro, na zakulo masu aikata laifi.
Dangantaka tsakanin makiyaya da manoma a jahar Filato ta fara armashi bayan da wani manomi mai suna Solomon a kauyen Bisichi dake karamar hukumar Barkin Ladi, ya yafe barnar da dabbobin wani makiyayi, Ibrahim suka yi masa a gonarsa.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.