Shugaban kungiyar raya al’ummar Tibi a jihar Nasarawa, Peter Ahemba ya ce a yammacin ranar Lahadi sun yi kirga gawarwaki hamsin da biyar.
“Kamar karfe 11 na dare wasu ‘yan bindiga wanda muna zaton su Fulani sun je sun shiga wani kauyen Tibi mai suna gidan Chabo, sun kashe sama da mutum ashirin. Da gari ya waye sai rikicin ya karu, yanzu haka ya shiga lafiya da Obi Local Government, waddanan kanana hukumomi biyu abin ya shafa." In ji Peter Ahembe
Ya kara da cewa sama da kauyukan Tibi 15 an ta da su daga muhallinsu, wadanda aka kashe daga rahotannin suka samu daga manya daga kauyukan sun kai 55, maza da mata, da kuma yara. Ana kokarin birni gawarwakin da aka samu.
Sai dai hukumomin tsaro ba su tabbatar da wannan adadi da suka mutu ba ko yawan garuruwan da aka tarwatsa kamar yadda Ahembe ya fada.
A gefe guda kuwa, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders a Jihar Nasarawa, Alhaji Dabo Bala Mohammad ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani bafulatani.”
“A shekaran jiya ne aka kashe wani bafulatani ya kai wa ‘ya’yansa makiyaya abinci, sun kira shi abincin su ya kare, ya nika gari ya kai musu, ya hau mashin yana hanyar sa ta dawowa a daidai wurin gidajen Tibi suka fito suka harbe shi a baya. Washegari kuma aka samu wasu da suka shiga inuwar wannan rigimar da ya faru, su ma su ka fada wa Tibi suka kashe su, wanda yake har yanzu mu ba mu iya tabbatar da su waye suka yi wannan abun ba.
Kazalika kokarin jin ta bakin hukumomin tsaro kan samun tabbacin cewa an kashe Bafulatanin kamar yadda Dabo Bala ya yi ikirarin, shi ma ya ci tura.
Sai dai a cewar Dabo Bala, "yanzu haka mun kira taron gaggawa na bangaren shugabannin Fulani da na Tibi domin tsawatarwa.”
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji: