Daukan matakin ya biyo bayan wani sako ne dake yawo a kafafen sada zumunta inda wasu gungun mutane ke shirin gudanar da zanga-zanga a yau Laraba, zuwa majalisar dokokin jahar Filato, kan kisan wasu matafiya da ake zargin wasu matasa da yi a cikin garin Jos ranar Asabar din da ta gabata.
Barista Lawal Ishay da ke zama darektan fasahar yada labarai da sadarwa na Jama’atul Nasril Islam a jihar Filato, ya ce sun gano takardar da ke dauke da kalaman da ke iya dagula al’amuran tsaro a jihar.
Ya kara da cewa, a matsayinsu na shugabanni sun san wadannan kalamomi masu iya haifar da fitina ne, shi ya sa suka yi kira ga jama’a.
"Barin wannan abu ya faru zai iya mayar da hannu agogo baya, kuma babu wanda ya nemi daga JNI wacce ke kula da babban masallaci na Jos." In Barista Ishaq.
A gefe guda kuwa rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato ta ja kunnen wadanda ke shirin yin zanga-zangar ne da cewa zasu dandana kudarsu idan har suka kaddamar da zanga.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji: