Rahotanni daga Filato da ke arewacin Najeriya na cewa Majalisar dokoki jihar ta tsige Kakakinta Abok Ayuba Nuhu.
Bayanai sun yi nuni da cewa an maye gurbinsa da Yakubu Sanda da ke wakiltar mazabar karamar hukumar Bassa.
Rahotanni sun ce ‘yan majalisar dokoki 16 ne cikin 24 suka tsige Abok. Rahotannin sun ce gabanin cire shi daga mukamin, an kusan ba hammata iska a tsakanin mambobin majalisar a zaman da ta yi don tsige shi a ranar Alhamis.
Wasu rahotanni kuma sun ce ‘yan majalisar da suka tsige kakakin wanda wannan shi ne karonsa na farko da ya shiga majalisar, ba su kai adadin da za su iya cire shi ba.
“Bayanai na cin karo da juna kan adadin mambobin majalisar da suka zauna don tsige Kakakin inda yayin da wasu ke cewa mutane shida, bakwai zuwa takwasa ne suka tsige shi wasu na cewa mambobi 17 ne akasarinsu ‘yan jam’iyyar APC.” Wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta ruwaito.
Bayanai sun yi nuni da cewa, mambobin majalisar da ke goyon bayan Abok sun boye sandar majalisar a wani yunkuri na hada tsige shi, lamarin da ya kai ga nunawa juna yatsa.
Tun da sanyin safiyar ranar Alhamis mazauna birnin Jos suka ga an tsaurara matakan tsaro a kewayen majalisar dokokin jihar ta Filato wani abu da ya yi nuni da cewa akwai ta a kasa.
Bayan kai ruwa rana da aka yi, a karshe majalisar mai rinjayen ‘yan jami’yyar APC mai mulki ta yi nasarar tsige shi ta maye gurbinsa da Sanda.
Tun kwanakin baya ne dai aka sami takun saka tsakanin kakakin majalisar da bangaren zartaswa bayan wasu kalamai da ya yi na nuna cewa gwamnati ta fito karara ta magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji: