A cigaba da yunkurin da kungiyoyin al’umma ke yi don bada gudunmowarsu kan yaki da batagari da samar da tsaro, kungiyar kwararrun maharba a Najeriya ta horadda jami’anta fiya da dubu daya.
Jami’iyyar APC a Jahar Nasarawa ta zargi uwar jami’iyyar da neman haddasa rudani da rarrabuwar kawunan ‘ya’yan jami’iyyar a Jahar, biyo bayan sauya sunayen wassu deliget da zasu gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan takarkaru.
Rundunar sojin Najeriya ta jaddada kwarewarta wajen kakkabe burbushin ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyi dake tada kayar baya da barazana ga tsaro a kasar.
Kungiyar hadin kan Kirista a Najeriya-CAN, reshen jahar Filato ta bukaci a rika yin hukunci kan duk wadanda suka aikata ba daidai ba, don samar da adalci ga kowa.
Shugaban kungiyar ta CAN a jihar Filato, Rabaran Fada Polycarp Lubo, ya ce za su gudanar da sujada da addu’o’i na musamman ne a ofishin kungiyar CAN.
Wasu mutane goma sha takwas dake neman takarar kujerar gwamnan jahar Filato a karkashin jami’iyyar APC, sun yi barazanar ficewa daga jami’iyyar tare da dimbin magoya bayansu, in har jami’iyyar bata dakile take-taken dora dan takara da basu amince da shi ba.
Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ya umurci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka kai hari kan Sanata mai wakiltar Filato ta kudu, Nora Dadu’ut da wasu ‘yan jarida goma sha uku.
Rundunar ta ce ta kwato makaman ne a lokuta daban-daban yayin gudanar da aikinta na tabbatar da zaman lafiya.
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta gano ma’adinan karkashin kasa fiye da talatin a Jihar, da take da yakinin sarrafasu zai janyo ingantan tattalin arziki da kawo saukin masifun rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Majalisar kolin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi afuwa wa tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame.
A yau Jumma’a ne al’ummar Kirista a fadin duniya ke fara gudanar da bukukwan Easter.
Bayanai daga wassu kauyukan karamar hukumar Kanam a jahar Filato na nuni da cewa mahara sun kashe mutane da dama a kauyukan dake yankin.
Rashin tsaro da ke ci gaba da lakume rayukan al’ummar Najeriya da haddasa asarar dukiyoyi da kara talauta ‘yan kasar, ya sa al’umma da daidaikun jama’a da ma kungiyoyin addinai ke ci gaba da janyo hankalin hukumomi kan su kara kaimi don kawo karshen rashin tsaron.
‘Ya’yan kungiyar Fulani mabiya Isa Almasihu sun jaddada batun hadin kan al’umma ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, wanda a cewarsu zai zama mafita ga matsalolin tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta.
Kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Bassa da ke jahar Filato, ta bukaci hukumomi su yi bincike kan wani sabon salo na kisa da ake yi wa dabbobinsu, ta hanyar sanya musu guba a ruwa da abinci.
Rundunar sojin Najeriya ta ce zata ci gaba da horar da jami’anta don tinkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta da zummar magance su.
Mata daga wasu yankunan da aka samu rikice-rikice a sassan jahar Filato, sun gano cewa kafa kungiyoyin fadakarwa kan zaman lafiya sun fara yin tasiri, ganin yadda aka samu kwanciyar hankali a yanzu.
Jami’iyyun siyasa a jahar Filato sun kuduri aniyar daura damara don shiga manyan zabubbukan da ke gabatowa a shekarar badi.
Ranar bakwai ga watan Fabrairun kowace shekara ne gwamnatin jihar Filato ta ayyana a matsayin ranar yafiya bisa rikice-rikicen da jihar ta fuskanta a baya.
A ci gaba da bikin ranar Hijabi ta duniya, mata da ‘yan mata a jahar Filato sun jaddada muhimmancin sanya Hijabi ga mace, don kare mutuncinta, da na addininta, da rage cin zarafin mata da ke yawaita.
Domin Kari