Kungiyar ta yi hakkan ne don taimaka wa jami’an tsaro da bayanai wajen gano maboyan ‘yan ta’adda da sauran bata gari a tsakanin al’umma.
‘Ya’yan kungiyar kwararrun maharban da aka tattaro su daga jihohin Kaduna, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Gombe, Adamawa da Filato sun yi kwanaki hudu, suna samun horo.
Sakataren kungiyar ta kasa kuma kwamandan kungiyar a Jahar Filato, Igem Danladi ya bayyana cewa, sun horar da jami’ian ne kan matakan kai rahoton matsalar tsaro cikin hanzari wa jami’an tsaro da kuma hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, a duk lokacin da suka ganta a daji.
Shima Sakataren kungiyar a Jahar Gombe, Danladi Muhammad Bage yace suna taimakawa ne, saboda karancin jami’an tsaro a Najeriya.
Malam Mohammed Yohanna daga Jahar Borno yace kungiyar tana samun nasara, inda ya kara da cewa ko cikin ‘yan kwanakin nan sun fafata da ‘yan kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane har sun kwato makamai da dama.
Kungiyar ta bukaci goyon bayan gwamnati da al’umma don samun kayan aiki da suka hada da motoci, babura da tallafin kudi don gudanar da aikin tsaron kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: