Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Miyetti Allah Ta Bukaci Gwamnati Da Ta Bincike Guban Da Ke Kashe Masu Dabbobi


Shanu
Shanu

Kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Bassa da ke jahar Filato, ta bukaci hukumomi su yi bincike kan wani sabon salo na kisa da ake yi wa dabbobinsu, ta hanyar sanya musu guba a ruwa da abinci.

Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah a karamar hukumar Bassa, Alhaji Ya’u Idris wanda ya bayyana cewa an sami zaman lafiya a yankin, da suke zaton zai dore, ya bayyana takaicinsa kan yadda a cikin kwanakinnan ake sanya wa dabbobinsu guba, suna mutuwa.

A bangare guda kuwa, mai magana da yawun kungiyar raya kabilar Irigwe, Mr Davidson Malison ya ce basu da masaniyar an sanya wa dabbobin makiyayan guba.

Shanu
Shanu

Ya kara da cewa yayin da aka kafa kwamitoci don sasanta yadda makiyayan za su shigo kasar Irigwe, wassu makiyayan sun shigo sun barnata amfanin gona wa manoman yankin.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su bada bayani kan lamarin ba, duk da sakon da murya Amurka ta aike wa STF.

Hukumomin gwamnatin jahar Filato da hukumar tabbatar da tsaro ta Special Task Force sun nada kwamitoci daban-daban don kawo karshen tashe-tashen hankula da ake samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankin na karamar hukumar Bassa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
XS
SM
MD
LG