A yankin Yalwan Gindin Akwati dake karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato da a shekarun baya aka kashe mutane da dama, matan yankin da suka hada kungiyar zaman lafiya suka ce gudunmuwar da kungiyoyi masu zaman kansu ke bayarwa ya taimaka wajen hada kan al’ummar yankin.
Wakiliyar Sashen Hausa ta kai ziyara a yankin inda ta samu kungiyoyin mata ta Musulmi da ta Krista, da ma kungiyoyin Hausawa da Fulani da sauran kabilu suna cudanya da juna sakamakon kwanciyar hankali da aka samu a yankin.
a hirar ta da Sashen Hausa, Malama Zuwaira shugabar kungiyar, ta ce gudunmuwar kungiyoyi masu zaman kansu wurin hada kan al’umma ya taimaka ainun. “Tun lokacin harin da aka kai a Yalwa, yanzu da muka samu kungiyoyin nan dai suna aiki, ana a tare nan a tare can, cikin ikon Allah abu ya zo da sauki,” in ji Zuwaira Isa.
Ita ma sakatariyar kungiyar Florence Tonshi, ta ce fadakarwar da suke yiwa junan su a kungiyar ta koyar dasu hakuri da juriya. Ta kara da cewa a baya tana cikin masu zafin rai da basu da yafiya, amma a lokacin da mijinta ya ga tana ba wasu hakuri ya bayyana matukar farin cikin sa ga wannan ci gaba da ta samu daga fadakarwar kungiya.
Suma matan kauyen Kakuruk dake yankin Gashish, da a baya ya kasance kamar fagen yaki, suka ce sun hada kai da sauran mabambantan addinai da kabilu don wanzadda zaman lafiya.
A kwanakin baya ma, matan yankin Miyango a karamar hukumar Bassa, sun hada irin wannan kungiyoyi da suka ce idan hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu zasu taimaka musu, za su ci gaba da fadakarwa da zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankunan nasu.
Ga rahoton Zainab Babaji daga Jihar Filato: