Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirista A Fadin Duniya Sun Fara Gudanar Da Bukukuwan Easter


Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bukukuwan Easter A Jihar Kano
Yadda Kiristoci Suka Gudanar Da Bukukuwan Easter A Jihar Kano

A yau Jumma’a ne al’ummar Kirista a fadin duniya ke fara gudanar da bukukwan Easter.

PLATEAU, NIGERIA - Bikin wanda ake gudanarwa kowace shekara ana farawa ne ranar Jumma’a, wanda ake wa lakabin ‘Good Friday ko Jumma’a mai kyau, zuwa ranar Litinin.

Mabiya addinin Kirista na yin bikin ne don tunawa da mutuwa da tashin Isa Almasihu, wanda suka yi imani ya mutu ne don ceton bil’adama daga shiga jahannama, matukar sun yi imani da farillansa.

Rabaran Ishaku Sule daga Bauchi ya ce Easter lokaci ne da masu bin Yesu Almasihu zasu sadaukar da kai wajen yin rayuwa da ta dace da yin addu’o’i don kasa ta zauna lafiya.

Wata Malama Hauwa Danjuma Bello ta ce kamata yayi mabiya Kiristi su nuna kauna ga kowa su kuma tallafa wa mabukata.

Wasu dake gudun hijira a garin Vom dake Jihar Filato sun bayyana cewa zasu yi bikin na Easter ne cikin bakin ciki, saboda kisa da ‘yan bindiga suke yi masu.

Duk da yanayi na tashin hankali da matsin rayuwa da ake fuskanta, mabiya addinin Kiristan dai sun ce zasu dukufa ga yin addu’o’i don Allah ya daidaita lamura.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Kirista A Fadin Duniya Sun Fara Gudanar Da Bukukuwan Easter
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

XS
SM
MD
LG