Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kara dankon dangantakarta da farar hula don fahimtar aiyukanta da samar da zaman lafiya a kasa.
Kusan makonni uku kenan tun bayan da wani rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje, yayin da mutanen kauyukan da ke kewaye da garin na Tattara suka yi gudun hijira zuwa garin Garaku, shalkwatar karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa.
Al’ummomin kauyen Tattara da sauran kauyukan da rikici ya daidaita a karamar hukumar Kokona a Jahar Nasarawa sun bukaci gwamnati ta samar musu da tsaro don su koma yankunansu su yi noma.
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin tankar man fetur a mahadar hanyar Bauchi, dake nan cikin garin Jos.
Sama da mako guda kenan rikice-rikice ke ta kunno kai a kananan hukumomin Mangu, Barikin Ladi, Bokkos da Riyom, lamarin da yayi sanadin rayukan gomman mutane, bacewar dabbobi da kone-konen gidaje.
Rundunar ‘yan sandan Jahar Nasarawa a arewacin Najeriya ta yi nasarar kama mutane goma sha bakwai da ake zargi da ayukan garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.
Mutane akalla tara sun rasa rayukansu biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin makiyaya da mutanen kauyukan yankin Tattara a karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa.
Wannan umurnin na zuwa ne bayan zanga-zangar da wasu mata suka kwashe mako guda suna gudanarwa don nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon zaben gwamna a jihar, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana gwamna mai ci Injiniya Abdullahi Sule na APC, a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kwanaki kalilan kafin zabubbukan gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki a wassu jihohin Najeriya, an fara samun zafafan kalamai daga wassu jama’a, wanda idan ba’a dakile su ba, za su iya janyo tashin hankali a tsakanin al’umma.
Kwanaki kalilan kafin zaben gwamnoni da ‘yan Majalisun Dokoki a wasu jihohin Najeriya, an fara samun zafafan kalamai wadanda masan ke ganin idan ba’a dakile su ba, za su iya janyo tashin hankali a tsakanin al’umma.
Rahotanni daga Jahar Binuwai na nuni da cewa mutane kimanin hamsin ne ‘yan bindiga suka hallaka a wassu kauyuka fiye da goma sha biyu, a karamar hukumar Kwande, dake Jahar Binuwai.
Zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a wannan shekarar ta 2023 ya hadu da tarin matsaloli da ke neman gyara kafin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki.
Farfesa Shehu Abdulrahman wanda ya sanar da sakamakon ya bayyana cewa jami’iyyar Leba ce ke kan gaba da kuri’u dubu dari hudu da sittin da shida da dari biyu da saba’in da biyu.
Rumfunan zabe da dama ne zasu ci gaba da gudanar da zabe a yau Lahadi a cikin birnin Jos, na JIhar Filato.
Zaben na shugban kasa da ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a fadin Najeriya, an gudanar lami lafiya a fadin Jahar Filato, in banda matsalolin rashin kai kayan aiki da wuri a wasu rumfunan zabe, lamarin da ya haifar da rashin fara zaben a kan lokaci.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najiriya ta bayyana cewa mutane miliyan casa’in da uku da dubu dari biyar da ishirn da biyu da dari biyu da saba’in da biyu ne suka cancanci yin zabe a zaben gama gari da za a gudanar a watannin Fabrairu da Maris na shekarar 2023.
‘Yan takarar kujerar gwamna a jihar Filato sun sha alwashin magance tarin matsalolin da jihar ke fuskanta in har suka samu nasarar lashe zabe.
Harin wanda ya auku da daren jiya Talata bayanai na nuni da cewa jirgin ya zazzago albarusai ne kan wasu makiyaya da suka biya kudi don fanso shanunsu daga wurin ‘yan sintiri da ke aiwatar da dokar hana kiwo da gwamnatin Benue mai makwabtaka da Nasarawa ta kafa.
Mabiya addinin Kirista sun yi bikin Kirsimeti tare da gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da samun shugabanni nagari a zabukan dake zuwa a shekarar badi.
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya umarci jami’an tsaro da su kamo ‘yan bindigan da suka hallaka mutum 11 a kauyen Maikatako da ke karamar hukumar Bokkos.
Domin Kari