Wata sanarwa daga shugaban karamar hukumar Mangu, Mr. Minista Daput ta ce daukar matakin ya biyo bayan wani hari da aka kai kan kauyukan Kubat da Fungzai wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
Kansila mai wakiltar yankin, Plangji Mwesh yace a lokacin da ya ke magana, rikicin ya bazu zuwa kauyuka da dama don haka basu da adadin wadanda suka hallaka.
Shugaban matasan Bwai, Dafet Clifford yace ya ga gawarwaki hamsin da daya.
A gefe guda kuma, shugaban kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono yace an hallaka mutanensa da dabbobi dama, wadansu na can suna neman agaji.
Tuni da gwamnan Jahar Filato, Simon Lalong ta bakin hadiminsa, Makut Simon Macham ya fitar da sanarwar umurtar jami’an tsaro su gagguta kamo wadanda suka aikata kisan don hukunta su.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto hukumomin tsaro ba su fidda wata sanarwa kan batun ba.
Saurari rahoton a sauti: