Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

USAID Ta Horar Da Manema Labarai Matakan Yada Labarai Da Zasu Habaka Zaman Lafiya


Taron USAID da CIPP
Taron USAID da CIPP

Hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Amurka tare da hadin gwiwar kungiyar Mercy Corps da kungiyar dake wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, CIPP ta horar da manema labarai matakan yada labarai da zasu habaka zaman lafiya da inganta zamantakewar al’umma, maimakon haddasa gaba da kiyayya.

Jami’in dake aiki da kungiyar Mercy Corps dake wanzad da zaman lafiya, Mr Godwin Okoko yace ‘yan jarida na kan gaba wajen yaki da rikice-rikicen da ke aukuwa a Najeriya, don haka suka tallafa wa ‘yan jarida na Jahar Filato kafa wata kungiya da zasu taimaka wajen yayata labaran da zasu kawo hada kan jama’a.

Taron horarwar wanda ya janyo ‘yan jarida dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jahar Kaduna, sun ba juna shawarwari kan yadda zasu gudanar da ayyukansu bisa ka’ida.

Ibrahima Yakubu, wakilin Radiyo DW ta kasar Jamus a Kaduna yace taron bitar na da tasiri wajen inganta aikin jarida, musamman a bangaren zaman lafiya.

Mr Josiah Buzun, wakilin Rediyo Najeriya yace taron bitar ya kara fadakar da shi yadda zai yi rahoto ba tare da ya tada hankalin jama'a ba.

Malam Adamu Baba dake aiki da kungiyar dake sasanta tsakanin addinai, yace taron ya bashi damar fahintar yadda zai yi aiki da ‘yan jarida wajen hana aukuwar tashin hankali tun daga matakin unguwanni.

Bayan kammala taron bitar an kuma kaddamar da kungiya ta ‘yan jarida da za ta taimaka wajen yada sahihan labarai da zasu hada kan kasa.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG