Bangaren shugaban majalisa Ibrahin Balarabe Abdullahi sun gudanar da zaben kakakin majalisar a babban dakin taro na ma’aikatar kananan hukumomin jihar saboda dalilan tsaro a cewar su, su kuma bangaren Daniel Ogah Ogazi suka gudanar da nasu zaben a majalisar dokoki bayan da suka kutsa majalisar. Sai dai ba tare da magatakarda na majalisar ya rantsar da shi ba.
Mamba mai wakiltar Keana a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Mohammed Adamu Omadefu, ya bayyana cewa tun farko jami’iyya da masu ruwa da tsaki kan ba da shawara kan wanda ya dace ya zama kakakin majalisa don samar da ci gaba.
A bangare guda kuwa, Daniel Ogah Ogazi wanda ke ikirarin zama kakakin majalisar yance sun bi ka'idodin doka.
Mai fashin baki kan harkokin yau da kullum, Barista Yusuf Shehu Usman, ya ce bangarorin biyu sun saba wa doka kuma hakan na iya shafar harkokin ci gaban al’umma.
Al’umma da suka wahala wajen zaben shugabanninsu na fatan ganin wakilan sun aiwatar da dokokin da zasu kawo zaman lafiya da ci gaba ta fannoni dabam dabam.
Saurari rahoton cikin sauti: