PLATEAU, NIGERIA - Rikicin ya faro ne da hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa kan mutane a kauyuka, wanda daga bisani ya rikide zuwa na kai hari da ramuwar gayya tsakanin al’ummomin yankin da a baya ke zaman lafiya da juna.
Shugaban riko na karamar hukumar Mangu Hon. Markus Artu, ya ce harin na baya-bayan nan ya yi sanadin rasa rayuka, a saboda haka aka sanya dokar hana fita da shiga garin na Mangu.
Wannan doka ta hana yawo a karamar hukumar Mangu ita ce karo na biyu a kasa da wata guda.
Jami’in kungiyar da ke wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa, wato Mercy Corp, Mr. Godwin Okoko ya shawarci al’ummar yankin da su yi hakuri da juna.
Shi ma Malam Abdullahi Gambo dake aiki a kungiyar da ke sasanta tsakanin makiyaya da manoma mai suna Pastoral Resolve, ya ce ya kamata jama’a su lura cewa wasu marasa son zaman lafiya dake amfana da rikicin ne ke tunzura mutane.
Bayanai na nuni da cewa fiye da mutane dari biyu ne suka rasa ransu a hare-haren da ‘yan bindigar suka kai kan al’ummar yankin a kauyuka da rugage fiye da hamsin, a cikin wata guda.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna