Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce kashe-kashen dake aukuwa a jihar ta'addanci ne tsantsa da wasu ke aikatawa akan jama'ar jihar, kuma dole a tinkare shi akan ayyukan ta'addanci, idan har ana so a yi nasarar dakatar da kisan mutane da barnata dukiyoyi.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da wata runduna ta musamman da za ta yi yaki da batagari da ke kashe-kashen rayuka da barnata dukiyoyin jama’a a jihar Filato.
Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin zakulo wadanda suka halaka mutane fiye da dari a karshen makon jiya, a jihar Filato.
A wata sanarwa da kakakin 'yan sandan jahar Filato, DSP Alfred Alabo ya aikewa manema labarai a yau Talata, ta nuna cewa 'yan bindigar da har yanzu ba'a sansu ba, sun kona gidaje 221, sun kuma kona babura 27 da motoci guda takwas.
Mabiya addinin na Kirista da Musulmi sun jaddada muhimmancin hadin kai da daina nuna wa addinan juna kyama da tsangwama don samun ci gaba da wanzarda zaman lafiya.
Komishinan Sufuri a jihar Filato, Davou Gyang Jatau yace gwamnati za ta farfado da dokar da zata tantance masu amfani da kekunan NAPEP da wadanda suka mallake su, ta hanyar amfani da na'urori na zamani.
Biyo bayan nasara da ya samu a kotun daukaka kara, Ministan Kwadagon Najeriya, Simon Lalong, ya yi murabus daga mukaminsa na minista inda ya tsallaka zuwa majalisar dattawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kwanaki goma sha shida don yin gangamin yaki da cin zarafi da ya jibanci jinsi, walau mata ko maza a fadin duniya.
Jami'ar tarayya dake Jos a jihar Filato ta kaddamar da katafaren sashe da zai kula da cututtukan koda, mafitsara, mahaifa da sauran cututtuka marasa yaduwa.
An rantsar da dan majalisa mai wakiltar Kokona ta Gabas a Majalisar Dokokin jihar Nasarawa, Danladi Jatau na jami'iyyar APC a matsayin sabon Shugaban Majalisar Dokokin jihar.
Kotun daukaka kararrakin zabe dake zama a Abuja ta warware sakar da kotun sauraren kararrakin zabe a jahar Nasarawa tayi, inda ta ayyana gwamna mai ci, Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jahar.
Rundunar tsaron Najeriya ta 'Operation Safe Haven' ta sha alwashin kwato makamanta da wasu bata-gari da suka kwace a karamar hukumar Bokkos a Jahar Filato.
Rundunar sojin Najeriya dake aikin samar da tsaro a jihar Filato, wato 'Operation Safe Haven', ta damke daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan Ardon yankin Panyam a karamar hukumar Mangu, Alhaji Adamu Idris Gabdo.
Kungiyar da ke sasanta tsakanin addinai reshen jihar Filato ta ja hankalin majalisar shari’a ta kasa, a kan ta maida hankali wajen yin nazarin yadda kotunan sauraron kararrakin zabe ke gudanar da shari’u, da a ganinsu ke cike da kurakurai, don kaucewa tashin hankali.
Kotun daukaka kara dake zama a Abuja, ta soke zaben Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Simon Mwadkon dake wakiltar jihar Filato ta Arewa a karkashin jami'iyyar PDP.
Masu ruwa da tsaki a jihar Nasarawan Najeriya sun yi kira ga al’ummar jihar da su maida wukakensu cikin kube, bayan musayar kalamai daga magoya bayan jami’iyyar APC da PDP a jihar, biyo bayan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Benue ta tabbatar da sace kwamishinan sadarwa, al’adu da yawon shakatawa na Jihar, Mr. Mathew Abo.
Kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Filato, ta yi watsi da karar da jami’iyyar APC ta shigar a gabanta, inda ta kalubalanci sahihancin zaben Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP.
Jami’iyyar PDP a jihar Filato ta ce lauyoyinta sun fara shirin daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a jihar, inda ta kwace kujerun sanata guda da ‘yan majalisun tarayya da suka yi nasara a karkashin jami’iyyar ta PDP.
Wasu daliban jami’ar Jos sun gudanar da zanga-zangar gargadi cikin lumana, inda suka bukaci hukumomin jami’ar su rage kudin makaranta da kuma bukatar ganawa da shugaban jami’ar don bayyana masa bukatunsu.
Domin Kari