Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Kwamishina A Jihar Benue


Rundunar 'yan sanda
Rundunar 'yan sanda

Rundunar ‘yan sandan Jihar Benue ta tabbatar da sace kwamishinan sadarwa, al’adu da yawon shakatawa na Jihar, Mr. Mathew Abo.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Madam Sewuese Kate Anene, a wani takaitaccen sako da ta aike wa wakiliyar Muryar Amurka ta kafar Whatsapp, ta ce ‘yan sanda sun fara binciken inda ‘yan bindigar suka kai kwamishinan.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun je gidan kwamishinan ne a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum, a daren Lahadi inda suka yi awon gaba da shi a kan babur.

Wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace tsohon shugaban karamar hukumar Ukum a ranar Asabar kafin a ranar Lahadi suka sace kwamishinan, duk a cikin garin na Zaki Biam.

A wata sanarwa da sakataren hulda da manema labarai na gwamnan Jihar Benue, Tersoo Kula ya rabawa manema labarai ya bayyana cewa gwamnati tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na aiki tukuru don ceto wadanada ke hannun ‘yan bindigar.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai hukumomi ba su gano inda kwamishinan da tsohon shugaban karamar hukumar ta Ukum suke ba, kuma ‘yan bindigar ba su kira iyalansu don neman kudin fansa ba.

Jihar Benue da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya dai ta sha fama da matsalolin tsaro daban-daban da suka hada da rikicin makiyaya da manoma, hare-haren ‘yan bindiga, rikicin kabilanci da sauransu.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG