‘Yan Majalisar sun zabi Jatau ba tare da hamayya ba, bayan kwanaki uku da korar tsohon kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi.
An rantsar da Mohammed Oyanki mai wakiltar Doma ta Arewa (PDP) a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
Oyanki, mai shekaru 26, shi ne dan Majalisa mafi karancin shekaru.
Tun farko kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori tsohon kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi.
A wani hukunci da ta yanke a ranar Talata, kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Sa’ad Ibrahim, a matsayin sahihin zababben dan Majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Umaisha/Ugya da aka yi a ranar goma sha takwas ga watan Maris na shekara ta dubu biyu da ishirin da uku.
Dandalin Mu Tattauna