Hukumomin jamhuriyar Nijar sun jagoranci aikin kona hodar iblis sama da kg 200 da aka kama a farkon watan nan na Janairu a hannun wani magajin gari lokacin da yake kokarin shigar da ita kasar Libya.
A Jamhuriyar Nijar, wasu kungiyoyin fafutuka sun kudiri aniyyar gudanar da zanga zanga a ranar Lahadi 30 ga watan Janairu da nufin nuna rashin gamsuwa da yadda al’amura ke gudanar a kasar, misali yadda mahukunta suka gaza shayo kan matsalolin tsaron da suka addabi jama’a.
A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin fafitika sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi 30 ga watan Janairu da nufin nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da al’amuran mulkin kasar.
Rahotanni a Burkina Faso na cewa sojoji sun dauki wani abu da ya yi kama da juyin mulkin kan gwamnatin kasar, inda suka tsare shugaban kasar Roch Kabore tare da neman sauyi ga sojoji da yakin da suke yi da 'yan ta'adda.
A Jamhuriyar Nijar mutane sun fara gargadin hukumomi su sauki matakai bayan da wasu rahotanni suka ayyana cewa ‘yan ta’addan Mali sun fara tsallakawa zuwa wasu sassan jihar Tilabery da nufin tserewa luguden wutar da suke fuskanta daga dakarun kasar.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar rage kudaden awon motocin da ake shigorwa kasar daga turai da nufin ba jama’a damar sayen motoci masu karancin shekaru yayinda a wani bangare matakin ke hangen bunkasa kasuwancin motoci.
Rasuwar tsohon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita mako guda bayan takaddamar da ta kunno kai tsakanin ECOWAS da gwamnatin rikon kwaryar ta Mali ta janyo aza ayar tambaya dangane da makomar takunkumin da kungiyar ta kakabawa Mali.
A jamhuriyar Nijer, masu aikin jigila sun koka a game da tsayawar harakoki bayan da hukumomin sufuri suka rufe iyakar kasar da makwabciyarta kasar Mali.
Masana sha’anin tsaro sun bayyana fargaba akan yiyuwar fuskantar koma baya a game da yaki da ta’addanci a yankin Sahel sakamakon matakin rufe iyakoki da kungiyar ECOWAS ta yi saboda saba alkawalin shirya zabe da gwamnatin rikon Mali ta yi.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kara jaddada aniyar ci gaba da bibiyar shari’ar nan ta mutanen da ake zargi da handame kudaden makamai a ma’aikatar tsaron kasar bayan bayyanar wasu takardun dake nunin hukumomin Nijar sun janye daga wannan shari’a.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta gabatar da wasu mutane da ta kama dauke da kilogram (kg) sama da 200 na hodar iblis da aka loda a motar magajin garin Fachi dake jihar Agadez a Nijar a lokacin da suka yi kokarin ketarawa zuwa kasar Libya.
A Jamhuriyar Nijar, wata kungiyar Fulani ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yadda ake zargin Fulani da hannu a ayyukan ta’addanci da na ‘yan bindigar da suka addabi jama'ar wasu yankunan kasar saboda haka suka bukaci hukumomi su gagauta daukan matakai don kaucewa barkewar rikicin kabilanci.
Lauyar dake kare ‘yan Rwandar nan da gwamnatin Nijar ta kora daga kasar ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira rashin mutunta alkawuran da kasar ta dauka a yarjejeniyar da suka cimma da MDD akan batun bai wa wadanan mutane mafaka.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kori wasu ‘yan Rwanda daga kasar saboda dalilan da aka bayyana a matsayin na diflomasiya, sai dai wasu ‘yan rajin kare hakkin dan adam na ganin alamar keta hakkin dan adam a wannan lamarin.
Kungiyoyin ‘yan kasuwar Jamhuriyar Nijar sun bayyana farin ciki bayan da shugaban hukumar Douane ya umurci ma’aikatansa su dakatar da matsawa ‘yan kasuwa game da takardar izinin wucin gadin fiton kaya.
‘Yan bindiga sun kai tagwayen hare-hare a wasu tashoshin bincike a garin Makalondi dake jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso inda suka hallaka jami’an tsaro tare da kona motoci sannan suka arce da wasu motocin ‘yan sanda.
A yayin da rundunar tsaron Faransa ta bada sanarwar kashe shugaban reshen kungiyar IS a yankin Sahara Soumana Boura a wani harin hadin gwiwa da dakarun tsaron jamhuriyar Nijer, masana sha’anin tsaro na da ra’ayoyi mabambanta dangane da tasirin wannan nasara a yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
A jamhuriyar Nijer kungiyar AJSEM da hadin guiwar UNESCO sun shirya wani taro domin fadakar ‘yan jarida akan bukatar mutunta ‘yancin ‘yan cirani ta yadda za a daina amfani da kalaman da ke kama da na cin zarafin bakin haure a yayin bada labari
A Jamhuriyar Nijar shugabanin al’umar karkarar Lahari dake yankin Diffa sun bayyana damuwa dangane da yanayin da ayyukan hakar man fetur suka jefa su ciki inda gurbacewar muhalli ta shafi ayyukan noma da kiwo.
A jamhuriyar Nijar shugabannin al’umar karkarar Lahari dake yankin Diffa sun bayyana damuwa dangane da yanayin da ayyukan hakar man fetur suka jefa su ciki inda gurbacewar muhalli ta shafi ayyukan noma da kiwo, saboda haka suka bukaci hukumomin kasar su dubi wannan al’amari kafin abin ya tsananta.
Domin Kari