A jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiya sun bada sanarwar dakatar da tallafin kudaden tiyatar haifuwa da aka saba yiwa mata kyauta sakamakon wasu dalilai masu nasaba da tsarin aikin, amma kuma za a ci gaba da tsarin bada magani kyauta ga mata masu juna biyu da yara kanana.
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan majalisar dokokin kasar sun zargi kakakin majalisar Alhaji Seini Oumarou da taka doka sakamakon rashin ba su damar sauraren Ministan tsaro da takwaransa na cikin gida a game da abubuwan da suka faru a ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata a garin Tera.
Hukumar yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani aikin zuba ido akan ayyukan ‘yan sandan kula da zirga-zirga da nufin tantance zahirin abubuwa irin na cin hanci da ake zargin su da aikatawa.
Jami’an tsaro sun kama kusoshin wata kungiyar fafutika cikinsu har da wani dan kasar Faransa.
Hadin gwiwar sojojin jamhuriyar Nijar da takwarorinsu na Burkina Faso sun yi nasarar wargaza wani sansanin 'yan ta'adda dake kan iyakar kasashen biyu, lamarin da ya ba su damar kashe 'yan ta'adda kusan 100 tare da kama makamai da babura fiye da 200.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kama shugaban kungiyar hadin kan al’umar jihar Tilabery Amadou Harouna Maiga bayan da ya yi wasu kalamai dangane da zanga-zangar nan ta matasan da suka datsewa ayarin motocin sojan Faransa hanya a garin Tera a ranar 27 ga watan November 2021.
A yayin da kasashen duniya ke bukin tunawa da ranar yaki ta cin hanci a yau 9 ga watan Disamba, shugaban hukumar yaki da cin hanci a jamhuriyar Nijer, Mai shara’a Mai Moussa Alhaji Basshir ya bayyana cewa matsalar cin hanci na kara tsananta a ma’aikatun gwamnati.
Gwamantin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijer gudummuwar jirgin sama samfarin Hercules C 130 domin amfanin sojojin kasar a yakin da suke kafsawa da 'yan ta'adda.
Shugabannin al’umma a Jamhuriyar Nijar sun bukaci gudunmawa daga kungiyoyi masu zaman kansu wajen samar da ayyukan yi a karkara irinsu noman rani da nufin cire wa matasa tunanin zuwa kasashen waje.
Hukumomim jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar sojojin kasar 12 sakamakon harin da aka kai a kauyen Fantio na gundumar Tera a shekaran jiya asabar yayinda sojojin suka kashe gomman ‘yan ta’adda suka kuma kwace babura da dama da na’urorin sadarwa.
Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijer ya yaye wasu matasa kimanin 45 wadanda suka kammala daukan horon watanni 3 a kan dubarun kafa masana'antu da shugabancin harakokin jama'a kamar yadda aka saba a karkashin shirin tsohon shugaban Amurka Barack Obama.
Daliban Cibiyar Koyon Dabarun Kafa Masana'antu da Koyon Shugabanci kimanin 45 ne aka yaye a Jamhuriyar Nijer a wannan zangon a karkashin shirin da tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya bullo da shi don ciyar da kasashen Afurka gaba.
A janhuriyar Nijer, masu lalura ta musamman sun yi amfani da wannan rana tasu ne wajen godiya ga Allah da kuma yin addu'o'in samun zaman lafiya a kasar da ma duniya baki daya.
A yayinda ake shagulgulan tunawa da ranar yaki da bauta ta duniya a yau 2 ga watan disamba kungiyoyin yaki da bauta a jamhuriyar Nijer sun yi bitar halin da ake ciki game da wannan al’amari shekaru 70 bayan wannan yunkuri na kawo karshen wannan dabi’a.
A jamhuriyar Nijar masu shagunan kemis kemis wato pharmacie sun dakatar da aiki daga yau Laraba 1 ga watan Disamba har sai yadda hali ya yi.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya gana da shuwagabanin kungiyoyin addini inda ya bukaci gudunmowarsu wajen neman hanyoyin warware matsalar tsaron da ta addabi kasar da makwaftanta.
Tawagogin matasa daga kasashen G5 Sahel sun hallara a jamhuriyar Nijar don tattauna hanyoyin kafa wata majalisar matasan kasashen wannan yanki a ci gaba da neman hanyoyin kare matasa daga tarkon ‘yan ta’adda a wannan lokaci na yawaitar aika-aikar ‘yan bindiga.
Nan ba da jimawa ba Manoma da Makiyaya za su ga kokarin mahukunta a Jamhuriyar Nijar.
Domin Kari