Wannan lamari ya janyo martani daga ‘yan kasar ta Nijer.
A wani taron manema labaran da ya kira a karshen makon jiya a birnin Ougadougou na kasar Burkina Faso, kwamandan rundunar sojan Barkhane, Gen. Laurent Michon, ya tabbatar da cewa babu zancen girke dakarun tsaron rundunar ta Faransa a Nijer bayan ficewarta daga Mali, amma kuma sojan saman Faransar da ke da sansani a Nijer zasu ci gaba da zama a kasar ba tare da aiwatar da wasu sauye sauye ba.
Tsohon ministan tsaron Nijer bugu da kari dan majalisar dokokin kasa, Kalla Moutari, na mamakin jin wannan magana daga bakin wani hafsa.
Shugaban kungiyar farar hula ta voix des sans Voix Nassirou Saidou na mai danganta matakin na Faransa da yakin da Rasha ke gwabzawa da Ukraine a wani lokacin da gwamnatin Mali ta kafe akan bukatar ganin Faransa ta fice daga kasar.
Mu’amular aiki da rundunar hadin gwiwar kasashen Turai wato Takuba shine abinda ke gaban hukumomin Nijer a yau a maimakon cece kuce akan makomar Barkhane.
A nan kadan cikin watan nan na Maris ne majalisar dokokin Nijer za ta yi zamanta na shekara shekara domin nazari akan kudirorin dokar da bangaren zartarwar zai gabatar wato session des lois kuma akwai yiwuwar batun bai wa rundunar takuba izinin girke dakarunta a wannan kasa ya shiga sahun batutuwan da ‘yan majalisar zasu tattauna akansu kamar yadda shugaba Mohamed Bazoum ya Ayyana a ganawarsa da shugabannin al’umma a karshen watan jiya.
Saurari cikakken rahoton cikin a sauti: